Masar: Wasu ministoci biyu sun ketare rijaya da baya | Labarai | DW | 20.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masar: Wasu ministoci biyu sun ketare rijaya da baya

Sojojin kasar Masar sun kashe wasu mayakan kungiyar IS guda biyar wadanda suka kai hari a kusa da  filin saukar jiragen sama na Al-Arich da ke a arewacin yankin Sinai.

 

Kungiyar ta IS ta ce ta kai harIn ne da nufin kashe ministocin tsaro da na cikin gida na Masar da suka kai ziyara a yankin domin duba yadda harkokin tsaro ke tafiya. Rundunar sojojin ta Masar ta ce babu ko daya daga cikin ministocin da ya samu rauni, sai dai ta ce hafsoshin soji na gwamnati guda biyu sun mutu a sakamakon harbi wani makamin roka.