Masar ta zama zakara a Afirka | Zamantakewa | DW | 25.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Masar ta zama zakara a Afirka

Masar ta lashe kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka na 'yan kasa da shekaru 23 a yayin da daga nata bangare kasar Spain ta lashe kofin gasar kwallon tennis ta duniya ta Davis Cup.

A wasannin Bundesligar kasar Jamusa karshen mako aka buga wasannin mako na 12. inda yaya karama Borussia Dortmund ta yi sababalwa a gida inda da kyar da jibin goshi ta ceto kanta  agaban Paderborn inda suka tashi 3-3. Yaya babba Bayern Münich ta iske Dusseldorf har gida ta kuma casa ta da ci 4-0. Schalke04 ta doke Bremen da ci 2-1. Bayer Leverkuzen da Freiburg sun tashi ba kare bin damo da ci 1-1. Union Berlin ta mamayi

Mönchengladbach da ci 2-0, a yayin da takwararta ta Hertha Berlin ta kwashi kashinta a hannu a Augsburg da ci 4-0. Leipzig ta caccaki Kolon da ci 4-1, Hoffeinheim ta yi raggon kaya a gida a gaban Mayence wacce ta wulakantata da ci 5-1, sai kuma dukan da Wolfsburg ta yi wa Frankfurt a gidanta da ci 2-0 wasan da shi ne ma muka kawo maku kai tsaye a ranar Asabar da ta gabata: Atmo....

Har yanzu dai Kungiyar Mönchengladbach na ci gaba da kasancewa a saman tebirin na Bundesliga da maki 25, Leipzig na a matsayin ta biyu da maki 24, Bayern Munich na a matsayin ta uku da maki 24 ita ma.

A nahiyar Afirka inda a kasar Masar ta lashe kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka na 'yan kasa da shekaru 23 na shekara ta 2019. Masar ta lashe gasar karo na uku wacce ta karbi bakuncinta, bayan da a wasan karshe ta doke kasar Cote d'Ivoire da ci 2-1.

A birnin Madrid na Span an kamala gasar cin kofin kwallon tennis ta duniya ta Devis Cup ko Coupe Devis ta shekara ta 2019, wacce mai masaukin baki kasar ta Spain ta lashe bayan da a wasan karshe Rafael Nadal ya doke Denis Shapovalov da ci 6-3, 7-6 da kuma 9-7. Wannan shi ne karo na shida da Spain ke lashe kofin duniya na kwallon tennis ta Devis Cup.Bayan kammala wasan Captain na kungiyar ta Spain Rafael Nadal ya bayyana gamsuwarsa da wannan nasara yana mai cewa:

"Wannan mako ya kasance mai kayatarwa, domin mun ga abubuwa masu yawa, mahaifin wani abokin wasunmu ya rasu, wani daga cikin 'yan wasan namu ya ji rauni, to amma duk da haka daga karshe mun kasance a cikin farin ciki, kuma abubuwan da suka wakanana wannan filin wasan, lokaci ne da ba za mu taba mantawa ba a rayuwarmu"

A Demben zamani na duniya na WBC shahararren dan demben nan na kasar Amirka Deontay Wilder ya sake rike kambunsa na ajin masu nauyi bayan a jiya Lahadi a birnin Las Vegas ya kashe Luis Ortiz dan kasar Kuyba a turmi na bakwai bayan da ya kai shi kas a sakamakon wani bugon kawo wukka da ya yi masa a huska. Tuni ma dai 'yan demban biyu suka tsaida ranar 22 ga watan Febrairun sabuwar shekara domin sake gwabzawa.