Masar ta haramta ayyukan kungiyar ′Yan uwa Musulmi | Labarai | DW | 23.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masar ta haramta ayyukan kungiyar 'Yan uwa Musulmi

Ko da yake ana iya daukaka kara don kalubalantar wannan hukuncin, amma duk haka ya bude wa hukumomi kofar bin diddigin ayyukan jin kai da kungiyar ke yi.

Wata kotu a Masar ta haramta kungiyar 'Yan uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood sannan ta ba da umarnin kwace dukkan kadarorinta. Wannan hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar mai samun goyon bayan sojoji ke ci gaba da daukar matakan murkushe magoya bayan hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi. Gidan telebijin din kasar ta Masar ya ce a wannan Litinin kotun ta yanke hukuncin. Kungiyar 'Yan uwa Musulmi ta kasance karkashin takunkumi a mafi yawa na shekaru 85 na wanzuwarta. Amma bayan hambarar da shugaban kama karya Hosni Mubarak a shekarar 2011, an dage haramcin an kuma amince ta yi aiki a bayyane, inda ta kafa jam'iyyar siyasa har ta lashe zaben da aka gudanar bayan mulkin Mubarak. A watan Maris da ya gabata an yi mata rajista a matsayin wata kungiya da ba ta gwamnati ba. Ko da yake za a iya daukaka kara ga wannan hukuncin, amma ya bude wa hukumomi kofar bin diddigin ayyukan jin kai da kungiyar ke gudanarwa, kuma babban koma baya ne a gare ta.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal