Masar ta fitar da Hamas daga cikin ′yan ta′adda | Labarai | DW | 06.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masar ta fitar da Hamas daga cikin 'yan ta'adda

Wata kotun ɗaukaka kara ta soke wani hukuncin kotun wanda ya saka Hamas a cikin ƙungiyoyin 'yan ta'adda

Wani babban jami'n kula da harkokin shari'a a ƙasar ta Masar ya shaida wa manema labarai cewar an jingine hukunci ne domin kotun da ta zartar da shi ba ta da hurumin yin haka.

A ƙarshen watan Janairun da ya gabata ne kotun ta yanke hukunci a kan Ƙungiyar ta Hamas mai iko da Yankin Zirin Gaza na Falasɗinu kana kuma aka haramta wa ƙungiyar taɓa kuɗaɗenta na ajiya a cikin bankuna.Gwamnatin ta Masar na zargi Hamas da taimaka wa reshen Ƙungiyar IS a yankin Sinai wacce ke kai hare-hare a kan jami'an tsaro.Dangantaka tsakanin Hamas da Masar ta yi tsami tun bayan faɗuwar gwamnatin Mohammed Morsi a shekarun 2013.