Masar: Gobara ta kashe mutane 41 a coci | Labarai | DW | 14.08.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masar: Gobara ta kashe mutane 41 a coci

Wasu majiyoyi sun ce wutar lantarki ce sanadin tashin gobarar a lokacin da mutane akalla 5,000 ke addu'a a majami'ar a ranar Lahadi. Gwamnati ta kaddamar da bincike don gano tushen gobarar.

Rahotanni daga Masar na cewa fiye da mutane 40 sun mutu wasu 55 sun jikkata, sakamakon tashin gobara a wata majami'ar 'yan Kibdawa da ke birnin Giza a wajen Alkahira.

Kibdawa su ne mafi girma a cikin al'ummar Kirista a yankin Gabas ta Tsakiya, a kusan mutane miliyan 10 daga cikin adadin 'yan Masar miliyan 103.

‘Yan tsirarun dai sun sha fama da hare-hare tare da kokawa da nuna wariya a kasar Musulmi mafi rinjaye a arewacin Afirka, wadda ta fi kowacce yawan al'umma a kasashen Larabawa.