1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta nemi sakin masu zanga-zanga

Ramatu Garba Baba
September 24, 2019

Kungiyar Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin kasar Masar da ta gaggauta sakin kimanin mutane 500 da ta kame bayan gudanar da zanga-zangar adawa da Shugaba Al-Sisi.

https://p.dw.com/p/3Q8HV
Ägypten Kairo | Anti-Regierungsproteste
Zanga-zanga na ci gaba duk da haramcin gwamnatiHoto: Reuters/M. Abd El Ghany

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty ta yi kira ga mahukuntan kasar ta Masar da su gaggauta sakin kimanin mutane 500 bayan da ta ce kundin tsarin mulki ya bai wa ‘yan kasa damar yin hakan cikin lumana.

Wannan na zuwa ne, bayan wani umarnin toshe kafofin sada zumunta na yanar gizo, wadanda masu fafutuka ke amfani dasu wajen gayyatar ‘yan kasar dasu shiga gangamin zanga-zangar da suke shirin gudanarwa a ranar Juma‘a mai zuwa, da suka yi wa  take da ‘‘zanga-zangar ayi ta, ta kare‘‘ a wani yunkurin  ganin bayan mulkin Shugaba Abdel-Fatah Al-sisi.