Masar ta haramta buda baki a masallatai saboda Coronavirus
April 5, 2020Talla
Ma'aikatar kula da masallatai ta kasar ta ce ba za a ga irin haka a azumin bana ba, saboda takaita yaduwar Coronavirus. Hukumomi sun yi kira ga attajirai cewa a maimakon su tara cincirindon jama'a a lokacin shan-ruwa, zai fi kyau attajiran su rarraba wa gajiyayyu kayan abinci ko kuma su rarraba wa jama'a tallafin kudi.
A watan da ya gabata Masar ta sanar da rufe masallatai a wani mataki na dakile yaduwar Coronavirus wace kawo yanzu ta kama mutane 1,070 ta kuma yi sanadin mutuwar 71. Sai dai babu tabbas ko kasar za ta bude masallatai a watan azumin don yin sallar Tarawihi da sauran ibadu.