1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Marubuci Ngugi ya samu takardar Yabo

May 8, 2014

Jami'ar Bayreuth a nan Jamus ta baiwa sanannen marubucin adabin nan dan kasar Kenya, da ake kira Ngugi Wa Thiongo lambar digiri ta girmamawa.

https://p.dw.com/p/1BvIc
Ngugiwa Thiongo Autor Kenia
Hoto: A1 Verlag

Littafin da Ngugi Wa Thiongo ya rubuta mai suna "Weep not Child" a shekara ta 1964, shi ne na farko da marubucin daga yankin Afirka ta gabas ya rubuta da harshen Ingilishi. Thiongo ya sami iliminsa ne a jami'ar Makerere ta kasar Uganda, ya kuma sami karin ilimi mai zurfi a jami'ar Leeds a Ingila. Daga baya, duk da zurfin iliminsa na Ingilishi, ya yanke shawarar komawa rubuce-rubucensa da harshensa na asali, wato Kikuyu. Hakan kuwa ya biyo bayan wani abin da ya faru ne a shekara ta 1976, lokacin da shi da abokinsa a fannin rubuce-rubucen adadi, Ngugi Wa Mirii aka basu aikin rubuta wani wasa, da yan wasan kwaikayo zasu nuna a kusa da Nairobi, babban birnin kasar Kenya. Marubutan biyu suka yanke shawarar harshen da zasu yi amfani dashi domin rubuta wannan wasa. Ngugi Wa Thiongo yace:

Sanin gaskiyar cewar a wannan lokaci mun tambayi kanmu, shin da wane harshe ne ya kamata mu rubuta wasan kwaikwayon, ya zama shaidar dake nunar da yadda muka yi watsi da harshenmu, kuma muka yi nisa da asalinmu.

Yanke shawarar rubutu da harshen Kikuyu

Daga nan inji shi, shi da abokinsa suka yanke shawarar rubuta wasan kwaikwayon cikin harshen su na Kikuyu, wanda shine harshen da masu magana dashi suka fi yawa a kasar ta Kenya.

Saboda nasarar da wasan kwaikwayon ya samu, Ngugi Wa Thiongo ya fuskanci fushin gwamnati, saboda korafin cewar farin jininsa na ci gaba da karuwa, sakamakon kusantarsa da harshen da talakawan kasar suka fi fahimta, musamman a fannin wasannin kwaikwayo.

Har ya zuwa lokcin da Ngugi Wa Thiongo, ya yanke shawarar rubuta wasan kwaikwayo na farko cikin harshen Kikuyu mai suna Ngaahiika Ndeenda, ko kuma a takaice zan auri wanda nake so, rubutun adadi cikin wani harshen gargajiya na Afrika, wani bakon abu ne a nahiyar. Marubucin yace:

Ngugi wa Thiongo Ngugi wa Thiong'o Schriftsteller Afrika
Hoto: picture-alliance/dpa

Kyamar rubutun harshuna na Uwa

A game da ci gaban rubuce-rubucen adadi cikin harsunan Afrika, ana iya cewa manufofin gwamnatocin wannan nahiya a wannan lokaci sun tahallaka ne kan matakan ganin irin wannan manufa ba ta samu ci gaba ko yaduwa ba a rubutun adabi na Afrika.

Saboda haka ne komawar Ngugi ga rubuce-rubuce cikin harshen Kikuyu ya tayar da muhawara mai zafi a yankin na Afrika ta gabas. Masu adawa dashi sun hada har da marubucin adabi na Nigeria Chinua Achebe, wanda burinsa shine ya nunawa duniya cewar ya mallaki harshen yan mulkin mallaka kamar harshensa na asali.

Ngugi Wa Thiongo sannu a hankali ya lura da cewar ko da shike Kenya ta sami mulkin kanta, amma tana kara kasancewa karkashin mulkin kama karya. Hakan ya kaishi ga sanya kafar wando daya da mahukunta a wancan zamani, inda ma aka kamashi, aka azabtar dashi, aka kuma yiwa matarsa fyade. Ko da shike an kama wadanda suka aikata wannan laifi, amma Ngugi ya baiyana imanin cewar manufofinsa ne suka sanya shi gaba da yan siyasa, inda daga baya ya fice daga kasar. Sai a shekara ta 2004 ne bayan kare mulkin shugaba Daniel Arap Moi, sa'annan Ngugi ya koma kasarsa ta asali.

Jami'ar Bayreuth tace litattafan Ngugi, sun ba da gudummuwa domin fito da nahiyar Afika daga danniyar 'yan mulkin mallaka, musamman a fannin rubuce-rubuce cikin harsunan Afrika.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita : Usmane Shehu