1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'yan Najeriya kan jawabin Jonathan

February 25, 2014

Jawabin shugaban kasar dai ya tabo batutuwa masu yawa na boye da bayyane, a kokarinsa na kwantar da hankulan al'ummar kasar dake fuskantar rashin tabbas.

https://p.dw.com/p/1BF76
Goodluck Jonathan Präsident Nigeria ARCHIV 2013
Hoto: picture-alliance/AP Photo

A wani abun dake zaman kokari na kwantar da hankula a tarrayar Najeriyar da tai dumi shigen gidan gashin Buredi, shugaban kasar Goodluck Ebele Jonatahn ya share tsawon daren wannan Litinin ya na dumi yana saukewa da nufin bayyana al'amurran kasar daban daban. Kama daga na can cikin ruwa ya zuwa abun dake karkashin sama, dama wanda boye a can sama dai ya kai ga tabo kusan komai ga shugaban Najeriya dake kokarin kwantar da hankula dama sanya zukatun dake tafasa cikin kasar yanzu haka.

Ya dai tabo batun tsaro ya kuma yi nazari a bisa shekaru dari na tarrayar Najeriyar, kafin karkata zuwa ga babban taro na kasa dama dakatar da gwamnan babban bankin kasar duk dai cikin tsawon awa daya da kwata da shugaban kasar dake hirar sa ta farko ga 'yan kasar a bana.

Goodluck Jonathan da ya zauna ya kalli karuwa dumi da tashin hankali ga siyasa dama zamantakewar al'umar kasar dai ya ce daga ranar 10 ga maris mai zuwa dai 'yan kasar zasu fara zama da nufin nazari ga makoma dama tattauna batutuwan dake da tasiri ga kokarin kasar na cigaba. To sai dai kuma bai yi kasa a gwiwa ba wajen jaddada aniyarsa na tabbatar da cigaban kasar wuri guda har mahdi ya bayyana.

Nigeria Goodluck Ebele Jonathan Komitee zur Vorbereitung der Nationalen Konferenz
Hoto: DW/U. Musa

"Babu wani shugaban da zai zauna ya kalli kasarsa rushewa gida gida. Najeriya muna da kima da mutunci ne domin girmanmu da banbancinmu. Muna rabuwa zuwa kasa kasa to mun lalace kenan. Ina jin babu wani mai son raba Najeriya ya zamo abun batu yayin taron".

Ko bayan kwantar da hankula game da makomar kasar dake shirin share tsawon makon nan tana biki dama shagulgula na shekara dari, shugaba Jonathan din dai ya kuma koma makarantar lallashi da nufin wanke sunan sa bisa zargin dakatar da gwamnan babban bankin kasar na CBN da nufin boye batun rashawa da hancin da ta mamaye masana'antar man kasar ta Najeriya yanzu haka.

"In ka dubi batutuwan sun faro ne tun a watan Fabrairun bara har ya zuwa yanzu. Da farko dai Sunusi ya fara ne da batan dalar Amurka miliyan dubu 49.8. Hankalin kowa ya tashi, mun kuma samu wayoyi daga sassa daban daban na duniya cewar fa zai yiwu daukacin taimakon dake zuwa nahiyar Afirka a shekara zai salwanta cikin Tarrayar Najeriya, kamun daga baya ya kuma ya ce dala miliyan dubu 12 ne sannan kuma a karshe ya ce dala Miliyan 20, har yanzu ban san wanda ma nake iya kamawa ba.

Amma dai ku sani ko da dala daya ce ta salwanta a kamfanin man kasar na NNPC to kuwa sai mun gano."

A fadar shugaban dai, yana da iko na dakatar da gwamnan bankin amma kuma ya ce Sunusi na iya komawa kan kujerar sa da zarar an kamalla binciken da a cewarsa ke da muhimmancin gaske.

To sai dai kuma rai ya baci na shugaban da ya zargi wani gwamnan daga Borno da rashin godiya ga matakin gwamantin kasar na kai karshen matsalar tsaron dake zaman ruwan dare a daukacin sashin arewa maso gabas tare da kalubalantar Kashim Shetima da neman janye masa sojan, yaga abun da ke iya kaiwa ga biyo shi har fadar da yake takama da ita a birnin Maiduguri.

Nigeria Präsident Goodluck Jonathan Beerdigung Autor Chinua Achebe OVERLAY GEEIGNET
Hoto: Pius Utomi ekpei/AFP/Getty Images

"In har gwamnan Borno na tunanin sojan kasar ba su da amfani, to ya fada wa 'yan Najeriya ni kuma in janye sojojin daga Borno na wata guda kacal daga baya in koma, ya gani ko zai iya zama a fadarsa. Bai kamata a ce gwamna kamarsa na kalamai marasa amfani ba. Ga batun tura kantoman soja zuwa Borno kuwa to ka sani, Goodluck Ebele Jonathan bai san shugaban Najeriya yana shirin tura kantoma ya zuwa Jihar Borno ba.”

Ko bayan batun rashin tsaro shugaban da a baya ya tsara bayyana aniyarsa ta takara ko a'a a farkon shekarar da muke ciki dai, ya kuma waske ga batun takarar da ke raba kai a kasar tare da ayyana tasiri ga rayuwa a matsayin cancantar zabe maimakon sauyin shekar dake zaman ruwan dare a kasar.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar