1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin shugabanni a game da farmakin Israila a Lebanon

July 31, 2006
https://p.dw.com/p/BuoU

Shugabanin ƙasashe na duniya na cigaba da baiyana alhini da mummunan ɓarnar da Israila ta yi a Qana. Shugaban ƙasar Faransa Jacques Chirac ya yi Allah wadai da farmakin wanda ya ce ko kaɗan bai dace ba. Sakatariyar harkokin wajen Britaniya Margret Beckett ta baiyana taánnatin da cewa abin kaico ne, ta ƙara da cewa Britaniya ta sha nanata kiran Israila ta yi taka tsantsan. Shi kuwa shugaba Bashar al-Assad na Syria ya baiyana kisan kiyashin na Qana da cewa aikin taáddanci ne wanda aka aiwatar kuru-kuru a gaban manyan shugabanni na duniya. Sarki Abdallah na Jordan cewa ya yi wannan ɗanyen aiki ne Israila ta aikata. Yana mai cewa hakan ya saɓa dukkanin dokoki na ƙasa da ƙasa. Babban jamiín harkokin wajen ƙungiyar tarayyar turai Javier Solana, ya baiyana martanin shugabannin ƙasashen turai , yace ya yi matukar takaici da harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula waɗanda basu ba basu gani ba. Yana mai cewa babu wani abu da zai hujjata wannan aiki da Israila ta yi a Qana.