Martanin kasashen Turai kan harin Sweden | Labarai | DW | 07.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin kasashen Turai kan harin Sweden

Harin da aka kai kan babban birnin Sweden na janyo martanin kasashen duniya, musamman ma na yankin Turai da ke makwabtaka da kasar.

Kungiyar tarayyar Turai da sauran kasashen nahiyar sun bayyana goyon bayansu ga kasar Sweden, bayan wani hari da aka kai kasar. Da ranar wannan Juma'a ce dai wani ya kutsa cikin taron jama'a da babbar motar dakon kaya a tsakiyar birnin Stockholm inda bayanai ke nunin mutane 3 sun mutu wasu kuwa da dama suka ji raunuka. Gwamnatin kasar ta ce tana binciken wasu mutane 2 dangane da harin ta danganta da na ta'addanci.

Kakakin gwamnatin Jamus Steffen Seibert, ya yi tir da lamarin. Shi ma Shugaba Francois Hollande na Faransa ya nuna rashin jin dadin faruwar lamarin. Shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker, ya ce ya ji takaicin taba daya daga cikin kawatattun birane a nahiyar. Kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa a kasar ma ya sanar da dakatar da shiga da kuma fita tsakanin birnin na Stockholm a wannan Jumma'a.