1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Erdogan a kan boren 'yan Turkiya

June 3, 2013

Firaministan Turkiya ya zargin 'yan adawa da neman yi wa gwamnatinsa zagon kasa. Erdogan ya bayyana haka ne a wani jawabi kan zanga zangar da ya ke gudana a kasar.

https://p.dw.com/p/18ihl
An anti-government protester gestures during a demonstration in Ankara late June 2, 2013. Tens of thousands of people took to the streets in Turkey's four biggest cities on Sunday and clashed with riot police firing tear gas in the third day of the fiercest anti-government protests in years. Prime Minister Tayyip Erdogan blamed the main secular opposition party for inciting the crowds, whom he called "a few looters", and said the protests were aimed at depriving his ruling AK Party of votes as elections begin next year. REUTERS/Umit Bektas (TURKEY - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Türkei Proteste Regierung IzmirHoto: Reuters

Firaministan Turkiya Racep Tayyip Erdogan ya zargi 'yan adawan kasarsa da iza wutar jerin zanga zangogin kin jinin gwamnati da suka barke a wasu sassa na kasar. Cikin wani jawabi da ya yi ta kafar telebijin a jiya lahadi da maraice, firimiyan ya ce ba abin da ya hadashi da salon mulkin kama karya da 'yan adawa suka zarge shi da gudanarwa.

Dubban 'yan Turkyia ne suka fara fantsaka a kan titunan birnin Istanbul kafin na sauran sassa su bi sahunsu, domin tilasta wa gwamnati lashe amanta game da shirinta na sabbin gine gine. Sai dai Erdogan ya danganta hanyar da suka bi wajen nuna rashin amincewarsu da yunkuri gurganta demokaradiya.

"Sun lalata abubuwa da dama tare da fasa tagogin wasu shaguna. Wai shin wannan ne demokaradiya? suka ce Tayyip erdogan dan kama karya ne. Idan ko suna kiran mutumin da ya sadokar da rayuwarsa wajen bauta wa kasarsa mai mulkin danniya, to ba ni da ta cewa."

Firaministan na Turliya Erdogan ya kuma kare jam'iyar da ke kan karagar mulki da zargin da ake yi ma ta na amfani da karfin ikonta wajen mayar da kasar kan tafarkin addinin musulunci tsantsa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Saleh Umar Saleh