1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Jamhuriyar Benin ya samu wa'adi na biyu

April 14, 2021

Ana ci gaba da mayar da martani a Jamhuriyar Benin tun bayan sanar da cikakken sakamakon babban zaben shugaban kasar da aka gudanar inda Shugaba Patrice Talon ya samu nasara.

https://p.dw.com/p/3s00P
Wahlen in Benin I Patrice Talon
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Mataimakiyar shugaban hukumar zabe ta jamhuriyar Benin Boko Nadjo ta bayar da sanarwar sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar, wanda ya bai wa shugaba mai ci Patrice Talon nasara da gaggarumin rinjaye.

Wahlen in Benin I Patrice Talon
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Karin Bayani:Zaben Benin: Patrice Talon na iya samn nasara

Hukumar zaben ta CENA a sakamakon da bayyana, shugaba Patrice Talon da mataimakiyarsa sun lashe zaben da kaso 86.4 na kuri'un da aka kada, wanda tuni yan adawa suka sa kafa suka yi fatali da sakamako tare da cewa dama sun san a rina. Sai dai a nasu bangaren jim kadan bayan sanar da sakamakon magoya bayan shugaban sun barke da sowa tare da hawa titunan birnin Porto Novo fadar gwamnatin kasar.

Benin Cotonou | Verkündung Wahlergebnisse durch Wahlkommission CENA
Hoto: Séraphin Zounyekpe/DW

Dama dai an zargi gwamnati da kokarin yin magudi tun lokacin da wata zanga-zanga da ta barke, inda 'yan adawa suka toshe tituna a yankunan arewaci da tsakiyar kasar ta Jamhuriyar Benin wuraren da suke fada a ji wanda ya yi sanadiyar jinkirin isar kayayyakin zabe a mazabu da dama. Ernest Bai Koroma shi ne ya jagoranci tawagar masu sa ido ta kungiyar habbaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ya yaba wa hukumar zaben kasar duk kuwa da 'yan kurakuran da aka samu.

Karin Bayani:An hallaka masu zanga-zanga a kasar Benin
Haka zalika yan adawa na ta yada wasu faya-fayen bidiyo da ma na saurare a kafofin sada zumunta na zamani da ke nuna yadda aka yi magudi tare da satar akwatin zabe, inda suka zargi jami'an hukumar da hannu a dukkanin rashin gaskiyar da aka shirya wanda ya sanya shugaban hukumar zaben ta kasa ta CENA Emmanuel Tiando mayar da martani bisa cewa suna sane da wasu hotunan bidiyo da kuma muryoyin da ke zagayawa a kafofin sada zumunta na zamani dangane da zargin tafka magudi a zaben da ya gabata, amma tuni hukumar zaben ta bude bincike kan wurin da abin ya faru da kuma ko su wanecne suka yi wannan aika-aikar.
Sai dai Shugaba Talon wanda shi ne ya lashe zaben hamdala ya yi dangane da nasarar da ya samu, wadda kuma ya danganta da ayyukan alherin da yake gudanarwa suka ba shi wannan nasarar, tare da nuna farin ciki.

Wahlen in Benin I Patrice Talon
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images