1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa gabannin zabe a Benin

Abdul-raheem Hassan
April 9, 2021

Ana cigaba da samun tashin hankali tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga kasa da sa'oi kadan kafin a fara zaben shugaban kasa a jamhuriyar Benin.

https://p.dw.com/p/3rnbf
Weltspiegel 08.04.21 | Benin | Demonstranten gegen Präsident Talon errichten Straßensprerren
Hoto: Yanick Folly/AFP

Hukumomi a Jamhuriyar Benin sun tabbatar da mutuwar mutum na biyu cikin masu zanga-zanga bayan da sojoji suka bude wuta don tarwatsa masu bore da suka tsare titi a tsakiyar kasar.

Wannan dai na zuwa ne kasa da sa'o'i 24 a gudanar da zeben shugaban kasa. Shugaba Patrice Talon da ya yi alkawarin wa'adin mulki daya yana cikin masu takara a gobe, sai dai yawancin manyan 'yan adawa na gudun hijira, yayin da wasu kuwa aka soke takararsu.

Matakin da ya haifar da zazzafar zanga-zangar gama-gari.