1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan rataye matasa 15 a Masar

Mahamud Yaya Azare
December 27, 2017

A karon farko a sabon tarihin siyasar Masar, an zartar da hukuncin rataya ga matasa 15 lokaci guda, bayan da wata kotun sojoji ta samesu da laifin kai hare hare kan sojoji da jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/2pzVU
Aktion gegen Folter und Todesstrafe
Hoto: Picture-alliance/dpa/W. Steinberg

Zartar da wannan hukuncin da ke zuwa a daidai lokacin da 'yan ta'adda a yankin Sinai ke kara kaimin hare-harensu kan jami'an tsaro da ma fararen hula, tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro, inji daya daga cikin lauyoyin gwamnati:

"Wannan hukunci ne da ke kan doka. Sun amsa wannan laifin da bakinsu, baya ga tarin shaidun da aka tara. Kowa ya kashe a kasheshi, haka ne zai sa kasa ta zauna lafiya.”

Karancin shekarun wadanda aka yankewa hukuncin dai ya sanya hatta masu goyan bayansa sun so da ai musu sassauci. Dangin wadanda aka ratayen da suka je karbar gawarwakinsu, sun yi ta jan Allah ya isa.

Ägypten - Todesurteil für elf Angeklagte
Wadanda aka tsare dai kan ga tashin hankali a Masar kamar wadannan a 2015Hoto: STR/AFP/Getty Images

Tuni dai kungiyar 'Yan uwa Musulmi ta soki hukuncin da ta ce na tsagwaron siyasa ce, ta na mai kira ga 'yan kasar su yunkura don kifar da Sisi tun irin wannan danyen hukuncin bai iso kan su ba. 

Kungiyar kare hakkin bil'Adama da ta yi tir da kisan, ta nemi da a soke kotunan sojojin, kana a rika tuhuma a sarari, don tabbatar da adalci.

Ita kuwa kungiyar lauyoyi mamakinta ta nuna da saurin gama shari'ar gami da zartar da hukunci. Su ma dai galibin 'yan kasar, da ke ci gaba da nuna kaduwarsu da hukuncin, sun nuna cewa an yi cuta, ganin cewa matasan kadan suka dora a shekaru ashirin na haihuwa.