Martani kan kifar da gwamnatin Masar | Labarai | DW | 07.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martani kan kifar da gwamnatin Masar

Tsohon Firaministan Birtaniya ya yaba da kawar da gwamnatin Mohamed Mursi da sojojin Masar suka yi

Tsohon Firaministan Birtaniya, Tony Blair ya ce sojojin kasar Masar ba su da zabin da ya wuce kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Mursi. Blair wanda ke zama manzon musamman na bangarorin hudu kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ya bayyana haka cikin rubutun da ya yi a wata jarida, inda ya ce zabi biyu suka rage ko kasar ta tsunduma cikin rikici ko kuma a kawar da Mursi.

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya yi gargadin cewa fito-na-fito tsakanin magoya bayan hambararren Shugaba Mursi da masu adawa da shi ka iya jefa kasar cikin yakin basasa.

Ranar Laraba da ta gabata sojojin karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Sisi suka kifar da gwamnatin Mursi, sakamakon boren jama'a. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya nemi ganin daidaita lamura a kasar.

A wani labarin fadar shugaban riko ta Masar ta ce wani lokaci a yau za a bayyana sunan sabon firaministan gwamnati. An samu rudani bayan da a jiya aka bayyana sunan Mohamed ElBaradei a matsayin wanda zai rike mukamin na firaminista. Amma har yanzu rahotanni na cewa shi ke kan gaba tsakanin wadanda ake tunanin bai wa mukamin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas