Martani kan cire dokar ta ɓaci a Masar | Siyasa | DW | 13.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani kan cire dokar ta ɓaci a Masar

Mahukuntan Masar sun mutunta hukuncin Kotu sun cire dokar ta ɓaci a ƙasar, sai dai wasu 'yan ƙasa na ganin cewa an ɗauki matakin dan daɗaɗawa ƙasashen yamma ne

Egyptian protesters flee after Egyptian police dispersed the demonstration that was calling for amending the constitution to allow fairer presidential elections, in downtown Cairo, Egypt, Tuesday, April 6, 2010. Egyptian police violently dispersed the demonstration, dragging protesters and throwing them into waiting police trucks, and confiscated the cameras of photographers and television crews. (AP Photo)

Gwamnatin riƙon ƙwarya a Masar ta janye dokar ta ɓacin da ta hana zirga-zirga, watanni uku bayan sanyata, da zimmar yaƙar ayyukan ta'addanci da tarzomar da ta ɓarke bayan tsige shugaba Mursi da sojojin ƙasar suka yi

Wannan umarni na dakatar da dokar ta ɓacin da wata kotu ta zartar, mahukunta sunce za a fara aiwatar da ita tun a yau laraba, sai dai kamar wata sanarwar da sojojin kasar suka fitar, za su cigaba da yin aiki da dokar ta ɓacin, saboda har yanzu umarnin kotun bai isa hannunsu ba

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sabbin mahukuntan suka gabatar da dokar yaƙar ta'addanci da dokar tsara yadda za'a dinga yin zanga-zanga waɗanda aka jima ana kace-nace kansu, matakin da masu fafutuka ke cewa kamar anyi ba a yi ba ne

Babu wata doka da zata ta sanyawa mutane kangi kan gudanar da zanga-zanga da bayyana fi shi ko damuwarsu, bayan mahalaccinsu ya riga ya basu wannan 'yancin. Kamar kowane shugaban kama karya, yakan ƙirƙiri dokar da zai halattawa kansa kisa, da daure, da ɓarna da rushe rushe

U.S. Secretary of State John Kerry participates in a joint news conference with Egypt's Foreign Minister Nabil Fahmy (2nd L) in Cairo, November 3, 2013. A day before Egypt's deposed Islamist president goes on trial, Kerry expressed guarded optimism on Sunday about a return to democracy in the country, as he began a tour partly aimed at easing tensions with Arab powers. REUTERS/Jason Reed (EGYPT - Tags: POLITICS)

John Kerry da takwaransa na Masar Nabil Fahmy a taron manema labarai

Martanin Amirka da Tarayyar Turai

Tun bayan sanya dokar ta bacin dai, sabbin mahukuntan na Masar da ke neman samun karɓuwa a wajen ƙasashen duniya, ke shan caccaka daga ƙasashe ƙawaye irin su Amirka da Tarayyar Turai, da kuma kungiyoyin masu fafutuka, lamarin da ya sanya wasu ke ɗaukar janya dokar, da wani matakin daɗaɗawa ƙasashen ƙetare da neman samun shiga wurinsu.

Musamman ma bayan da aka jiyo kakakin gwamnatin ta Amirka na jinjinawa ƙasar ta Masar kan janye dokar.

"Muna maraba da janye wannan doka, ko da yake, mun ga gwamnatin ta Masar na shirin maye gurbinta da wasu dokoki masu tsauri, muna fata, duk wata dokar da za a sanya ta samu amincewar yan ƙasa baki daya ba tare da nuna wariya ga wani bangaren ko tsangwamarsa ba"

Waiwaye adon tafiya

A demonstrator wearing symbolic chains and blindfold holds a partially-seen banner showing a skeleton, with writing in Arabic reading The people of Egypt next to a hangman's noose, with writing in Arabic reading Emergency, at a demonstration held against the nearly 30-year old emergency laws in front of the parliament building in downtown Cairo, Egypt, Tuesday, May 11, 2010. Egypt's government called Tuesday for a two-year extension of the country's controversial emergency law which has been in place since 1981 and gives police wide powers of arrest, but with some new limitations on police powers. (AP Photo/Ben Curtis)

Wani mai zanga-zanga yana kwatanta lahanin dokar ta ɓaci

Kadan dai ana iya tunawa, tun bayan sanya dokar ta ɓacin da ta biyo kifar da shugaba Mursi, jami'an tsaron ƙasar sun sanya kangi a gwagwarmayar da masu ƙin jinin juyin mulki ke yi, yadda har suka fasa zaman dirshan ɗin da ake a dandalin Rabi'atul Adawiyya da Annahdha, lamarin da ya kai ga halakar dubban magoya bayan hamɓarraren shugaban, kamar yadda jami'an tsaron sukai ta amfani da dokar wajen kakkamewa ƙusoshin ƙungiyar 'yanuwa musulmi da magoya bayan shugaba Mursi, waɗanda ake hasashen adadinsu ya ɗara dubu 30

ra'ayoyin 'yan ƙasar dai ya bambanta, dangane da janye wannan doka

"Na yi murna da dauke dokar,domin zata bamu dammar walwala. Akwai talakawa da dama dake takure saboda dokar"

""Ni kam so nake a cigaba da aiki da dokar, domin har yanzu akwai tashin hankali a gari. Yanayin tsaro bai gama kyautatuwa ba"

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Pinaɗo Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin