Maroko ta lashe kofin Afirka na CHAN | Zamantakewa | DW | 08.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Maroko ta lashe kofin Afirka na CHAN

An kammala gasar cin kofin kwallon kafa na matasan Afirka masu taka leda a gida wato CHAN a Kamaru, bayan an kwashe makakonin ana karawa.

Bari mu fara da gasar cin kofin kwallon kafa ta 'yan wasan Afirka masu taka leda a gida wato CHAN, inda tawagar kwallon kafa ta Moroko ta lashe gasar bayan ta lallasa Mali da ci biyu da nema a wasan karshe da suka fafata daren Lahadin karshen mako a birnin Douala na Kasar Kamaru.

Gasar cin kofin Afirka na 'yan kasa d shekaru 17 na kara yin zafi

Har yanzu dai muna a nahiyar ta Afirka, inda a ci gaba da  gasar share fage ta neman samun gurbi a gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka na 'yan kasa ta shekaru 17, a karshen mako aka barje gumi tsakanin Senegal da Gambiya, inda kuma Senegal din ta lallasa Gambiya da ci hudu da biyu. Kasar Saliyo ta lallasa Guinea Bisau da ci daya mai ban haushi, yayin da Saliyo din ta kwashi kashinta a hannua wajen Mali da ci biyar da nema. A wasa na gaba dai za a fafata tsakanin Senegal da Togo sai kuma Mali da Guinea Bisau. Tuni dai kasashen Najeriya da Aljeriya da Afirka ta Kudu da Zambiya da Yuganda da Tanzaniya da Côte d'Ivoire da kuma mai masaukin baki Moroko suka samu tikitinsu na zuwa wannan gasa.

Dusar kankara ta sa an dage karawa ta wasu wasannin Bundesliga 

Idan muka koma nahiyar Turai kuwa, a wasannin Bundesligar kasar Jamus, inda aka shiga mako na 20 a kakar ta bana. A karshen mako Bayern ta lallasa Hertha Berlin da ci daya mai ban haushi a wasan da suka fafata a ranar Jumma'a. A wasannin da aka buga a ranar Asabar kuwa, Borussia Dortmund ta sha kashi da ci biyu da daya a hannun Freiburg, Augsburg kuwa ta kwashi kashinta ne a hannun Wolfsburg da ci biyu da nema. Leverkusen kuwa ta yi wa Stuttgart cin kaca ne da ci biyar da biyu yayin da Mainz ta lallasa Union Berlin da ci daya mai ban haushi FC Cologne kuwa ta lallasa Borussia Mönchengladbach da ci biyu da daya. A wasan da DW ta kawo muku kai tsaye kuwa, Schalke ta ci gaba da zama kurar baya, inda ta ji babu dadi a hannun RB Lepzig ta da kai mata ziyara da ci uku da nema. A ranar Lahadi Frankfurt ta lallasa Hoffenheim da ci uku da daya, yayin da kuma dusar kankara ta tilasta dage fafatawar da aka shirya yi tsakanin Arminia Bielefeld da Werder Bremen. Har yanzu dai Bayern ce ke saman tebur a kakar ta bana da maki 48 yayin da Leipzig ke biye mata da maki 41, sai kuma Wolfsburg da maki 38 a matsayi na uku Frankfurt na matsayi na hudu da maki 36 Leverkusen ke biye mata a matsayi na biyar da maki 35.Annobar corona na janyo gagarumin kalubale ga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai. Rahotanni sun nunar da cewa Jamus ta ce ba za ta bar  kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta Birtaniya ta shiga kasar ba, sakamakon rufe kan iyakokinta da Birtaniya da ta yi saboda annobar coronavirus.

Sauti da bidiyo akan labarin