Manufofin cikin gida na gwamnatin Ehiopia bada nasaba da karancin abinci | Siyasa | DW | 15.11.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufofin cikin gida na gwamnatin Ehiopia bada nasaba da karancin abinci

siyasar kasuwanci da kuma matsalar yunwa a ƙasar Athiopia

default

Tsawon shekaru ƙasar Ethiopia ke noma nauín shukan da ake samar da mai daga gare su da kuma Furanni don kaiwa kasuwannin Duniya tare da samun kuɗin shiga maimakon nauín abinci, yayin da a waje guda jamaár ƙasar Miliyan shida suka dogara ga tallafin abinci daga ƙasashen ƙetare.

Kimanin kashi 85 cikin dari na alúmar Ethiopia manoma ne waɗanda rayuwarsu ta dogara ga ayyukan noma, a yankinsu dake fama da matsanancin fari. A halin da ake ciki gwamnatin Ethiopia ta kiyasta cewa mutane kimanin miliyan shida ne ke bukatar taimakon gaggawa na abinci. A yanzu ma dai tuni Bankin Duniya ya amince da tsabar kuɗi Dala miliyan 480 domin tallafawa yunkurin samar da abincin ga jamaá.

Sai dai kuma ƙungiyoyi da dama na kare hakkin bil Adama sun yi suka da cewa wasu daga cikin matsalolin da suka haddasa yunwar, manufofi ne na cikin gida suka haddasa su. Suka ce wannan ya hada da shawarar Bankin Duniya ga gwamnatin Ethiopia wanda ya sa ta shafe shekaru da dama tana noma dangin amfanin gona da zaá kai waje don samun kudi maimakon noma abinda zata ciyar da jamaarta

FAO Welternährungstag in Äthiopien

Awash- Ethiopia.

A shekaru biyu da suka wuce baki daya damuna bata kai ba a kasar ta Ethiopia. Baranazar fari da kasar ke fuskanta ba wai ya dogara ne kadai akan karancin ruwan sama ko kuma tasirin sauyin yanayi ba, har ma da rashin ingantaccen tsarin noma kamar yadda Ulrich Delius na kungiyar cigaban alúmomi dake fuskantar barazana ya baiyana.

Babbar matsalar ita ce kananan manoma da dama sun rasa gonakinsu, ta hanyar jamián gwamnati wadanda suka tilasta musu bada gonakin a kudin da bai taka kara ya karya ba, domin abinda suka ce kasashen duniya zasu zo su zuba jari. A maimakon haka sai ake amfani da gonakin wajen noma abinda ake iya tatsar man da zaá yi makamashi da shi hakazalika da kumma furannin da ake jigilarsu zuwa kasashen turai da kuma Asia.

A yanzu dai kasar Ethiopia ita ce kasa ta biyu a Afrika da aka fi shuka furanni ko kuma Flawa da ake kaiwa nahiyar turai. Tun bayan da aka bullo da dashen Fulawoyin a shekara ta 2000. Matakin da ya sa daruruwan manoma yan kabilar Oromo dake kusa da birnin Addis Ababa suka rasa gonakinsu ba tare da an biya su wata cikakkiyar diyya ba.

Ulrich Delius yace bai dai kamata noma furanni da nauin sinadarn da ake makamashi da su ya kassara noma abincin da jamaá zasu ci ba. Alal misali yace a yanzu makiyaya lardin Afar sun rasa kashi 80 cikin dari na kasar nomansu mai yawa a yankin Awash ga noman rake. Yace akalla an jingilar da gona mai fadin hecta 330,000 a yankin kudanci da yammacin kasar dake fuskantar fari.

Dossier Internationale Menschenrechte - Kinder Hunger

" A da wadannan manoma kan noma abinda zasu ciyar da iyalansu, hasali ma dukkan abinda suka noma nasu ne, amma yanzu abin da ban takaici domin da kyar kake iya samun santi 5o ko Euro daya wanda ba zai isheka abinci yini guda da iyalinka ba.

Duk da wannan hali a yanzu gwamnatin Ethiopia na son jingilar da karin gonaki mai fadin hecta miliyan biyu da dubu dari bakwai ga masu zuba jari na kasashen ketare wadanda ke son noma irin shuka da ake yin mai na makamashi daga gare su. Tuni ma dai kamfanoni fiye da 2000 daga kasashen China da India da Saudiya da Jamus da sauran su suka zuba jarinsu ga wannan harkar noma.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala

Edita: Zainab Mohammed