Manhajar yaki da cutar daji | Himma dai Matasa | DW | 25.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Manhajar yaki da cutar daji

A kasar Yuganda wani dalibin kimiya ya dukufa wajen sarrafa wata manhaja da za ta taimaka wajen gano cutar daji na mama wato "Breast cancer

Shi dai Moris Atwine da David Mwesigway, dalibai ne a makarantar fasahar sadarwa. Sabon manjahar ta su na cikin tsigar safar hannu dauke da na'urar da ke gano cutar daji, wacce ake hada ta da wayar salular a matsayin kwakwalwar manhajar. Yadda cutar ke barazana ga rayuwar 'yan kasar na daga cikin abinda ya ja hankalin Moris ya kirkiro da manhajar.

" Na rasa 'yan uwa na ta dalilin cutar dajin mama, saboda haka ne na bullo da wannan dabarar. Sanin kowa ne dai cutar dajin mama ta zama ruwan dare a nahiyar Afrika, musamman a kasar Yuganda. Duk da cewa ana samun karuwar hayayyafa, to amma cutar na matukar ta'adi ga rayuwa"

Riga kafi dai aka ce yafi magani, to amma rashin samun likitoci na musamman shi ke zama babbar kalubale ga al'ummar da ke karkara, wanda ke haddasa jinkirin gano cutar. Dr. Dennis Mitti wani likita ne da ya yi tsokaci kan wannan manhajar da ke sauri gano cutar dajin mama.

“Zai yi matukar amfani, musamman idan ya shiga kasuwa, domin ba mu da karfin sayan na'urar tantance cutar daji da ma na'urar da ke daukar hoto. To amma wannan sabon manhajar, dai-dai ruwane daiden gari."

Kawo yanzu dai babu wanda zai iya sanin hakikanin karuwar cutar dajin mama a kasar Yuganda, to amma ana danganta ta da irin sauyin abincin da muta ke ma'amala da shi. A don haka ne ma masu fafutuka ke shirin gangamin wayarda kan al'umma, bisa mahimmancin saurin gano alamun kamuwa da cutar. Musamman ga wadanda ke rayuwa a karkara.

A yanzu dai kiwon lafiya shi ke zama babban kalubalen kasar Yuganda, kazalika hakan na zama babbar hanyar kasuwanci. Don haka ne ma wasu abokan Moris da David suka dukufa wajen kirkiro da manhajar gano cutar zazzabin maleriya da cutar tari. Kamar yadda matasan ke cewa a cikin ra'ayi mabanbanta.

“Da akwai yara masu baiwa da ke sha'ar fasaha, kuma ke aiyukan kirkire-kirkire.” “Wannan kuwa ya ce, akwai karancin kere-keren zamani, kuma kayayyakin ba su samuwa.” Wannan kuwa cewa ya yi“ Na yi la'akari duniya ta mana fintinkau, yayinda wasu na mataki na 10 a fannin ci gaba, mu kuwa an barmu a matakin farko.”

Bisa irin wannan ayyukan kere-keren zamani da matasan kasar Yugandan ke yi na taimako ga lafiyar al'umma, 'yan kasar na ganin samun madafa zai kara wa hazaka ga masu tasowa.

Sauti da bidiyo akan labarin