Mali za ta samu tallafi na kimanin dala 455 | Labarai | DW | 29.01.2013
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali za ta samu tallafi na kimanin dala 455

Masu bada agaji na kasashen duniya, sun yi alkawarin bayar da kimanin dalar Amirka milyan 455, domin aiyukan soja da jinkai a kasar Mali da ke yankin yammacin Afirka.

Masu bada agaji na kasashen duniya, sun yi alkawarin bayar da kimanin dalar Amirka milyan 455, domin aiyukan soja da jinkai a kasar Mali da ke yankin yammacin Afirka.

An cimma haka yayin taron baiwa kasar tallafi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda Amirka ta yi alkawarin bayar da dala milyan 96 da dakarun Mali da kuma na kasashen Afirka da ke kasar.

Kasashen Jamus da Sweden ko wacce ta yi alkawarin bayar da dala milyan 20 ga dakarun na yammacin Afirka, kuma Sweden ta kara dala milyan tara na aiyukan agaji. Kasar Japan za ta bayar da dala milyan 120 na aiyukan agaji.

Afirka ta Kudu dala milyan 10, Najeriya dala milyan biyar.

A wani labaran kasar Birtaniya ta bayyana shirin tura dakaru 240, zuwa kasar Mali da wasu kasashen Yammacin Afirka Afirka masu magana da harshen Ingilishi, domin aikin horaswa.

Sannan kasar ta ce za ta kara taimako ga dakarun Faransa da ke yakan kawar da kungiyoyin masu kaifin kishin Islama na arewacin kasar ta Mali. Kuma haka zai kawo yawan dakarun Birtaniya cikin nahiyar Afirka su haura 300.

Yayin da dakarun Faransa dana Mali su ka kwace diko da garin Timbuktu mai dadedden tarihi, anata bangaren a wannan Talata kungiyar Azbinawa ta ce ta karbi iko da garin Kidal, daga hanun mayaka masu kaifin kishin Islama.

Kungiyar ta Azbinawa ta bayyana haka lokacin da dakarun Faransa su ka dumfari birnin wanda shi ne na karshe da ya rage a hanun 'yan tawaye, domin kwacewa.

'Yan tawayen sun ce suna shirya da aiki tare da dakarun Faransa saboda kawar da masu kaifin kishin Islama. Yanzu haka kuma dakarun Afirka na ci gaba da daukan matakan karfafa zaman lafiya cikin yankunan da aka fatattaki 'yan tawayen.

A wani labarin a wannan Talata, mutane sun fasa shagunan Larabawa da ake dangantawa da 'yan tawayen na kasar ta Mali, inda su ka yi wasoson ganima. 'Yan jarida sun bayyana gano makamai cikin wasu shagunan da aka fasa a birnin na Timbuktu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh

 • Kwanan wata 29.01.2013
 • Rahotanni masu dangantaka Siriya
 • Muhimman kalmomi Syria
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17TXC
 • Kwanan wata 29.01.2013
 • Rahotanni masu dangantaka Siriya
 • Muhimman kalmomi Syria
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17TXC