1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali ta koka kan yarjejeniyar tsaro da Faransa

January 18, 2022

Firaminista Choguel Kokalla Maiga ne ya fara kokawa kan yarjejeniyar, inda ya ce an danne Mali a cikin yarjejeniyar, domin Mali ba ta da ikon amfani da jirgin sama a cikin kasarta ba tare da amincewar Faransa ba.

https://p.dw.com/p/45fZL
Mali Oberst Assimi Goita, neuer Übergangspräsident
Hoto: AP Photo/picture alliance

Gwamnatin mulkin soji ta kasar Mali ta gabatar wa kasar Faransa bukatar sauya yarjejeniyar samar da tsaro da ke tsakanin kasashen biyu.

Wani jami'in diflomasiyya na Faransa ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransan, AFP cewa Faransa ta fara nazarin bukatar sauye-sauyen da Mali ke bukata a yarjejeniyar da aka fara tun a shekara ta 2013.

A watannin baya-bayan nan dai alakar diflomasiyya a tsakanin Mali da tsohuwar uwar-gijiyarta Faransa, na ci gaba da tabarbarewa tun bayan da zargin wanzuwar sojojin hayar Rasha a Mali ya sanya Faransa fara tunanin janye dakarunta da ke taimaka wa Malin mai fama da hare-haren ta'addanci shawo kan lamarin.