1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun sake dage babban zabe a Mali

September 28, 2023

Gwamnatin mulkin sojan Mali ta dage zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a watan Fabarairun shekara ta 2024 da ke tafe, ta kuma dakatar da shirya zabukan majalisun dokoki da kananan hukumomi da kuma yankuna.

https://p.dw.com/p/4Wvdw
Mali | Assimi Goita | Shugaban Kasa | Gwamnatin Rikon Kwarya
Shugaban gwamnatin rikon kwaryar mulkin soja ta Mali Assimi GoitaHoto: Vladimir Smirnov/ITAR-TASS/IMAGO

Gwamnatin mulkin sojan Malin dai ta bayyana cewa ta dage zabukan na ranar 24 ga watan Fabarairun 2024 ne, saboda wasu gyare-gyare da take yi. Sai dai manazarta na hasahen cewar da wuya rashin tsaro ya bari a gudanar da zabukan. Wannan dai wani sabon jinkiri ne da aka samu a zaben, bayan alkawuran da ta dauka sakamakon matsin lamba daga kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO. Tun farko an shirya yin zagaye na farko na zaben a ranar hudu ga watan Fabarairu shekara ta 2024, kana a yi zagaye na biyu a ranar 18 ga watan. Sojojin sun yi juyin mulki har sau biyu a Mali cikin kasa da shekara guda, wato a watan Agusta na 2020 da kuma watan  Mayu 2021.

Mali I Zaben Raba-gardama | Kwaskkwarima | Kundin Tsarin Mulki
Sojojin sun yi zaben raba-gardama, domin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarimaHoto: Ousmane Makaveli/AFP/Getty Images

Tun da fari sun ce za su mika mulki ga farar hula a shekara ta 2022, amma a karshen shekarar ta 2021 gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin Kanal Assimi Goïta ta sanar da cewa ba za ta iya mutunta jadawalin da aka amince da shi da ECOWAS ko CEDEAO din ba. A cewarta tana tunanin kasancewa kan mulkin har zuwa tsawon wasu shekaru biyar, sai dai dalilan da gwamnatin ta bayyar kan dage zaben ba su gamsar ba. Yanzu haka dai kasar ta Mali na rasa sassa da dama na kasarta sakamakon yadda masu ikirarin jihadi suka katse hanyoyin da ke kai wa zuwa birnin Timbuktu da kewaye na arewacin kasar, abin da ya jefa dubban mazauna yankin cikin mayuwacin hali. A yankuna da dama na kasar ma, 'yan ta'addan na dada kai hare-hare. A halin da ake ciki gwamnatin rikon kwaryar Malin, ta ce nan gaba za ta bayyana sababbin ranakun zaben bayan tattaunawa da Hukumar Zaben Kasar.