1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali na juyayin kashe jami'anta na tsaro

August 11, 2022

Wasu hare-hare na karshen mako sun salwantar da rayukan jami'an tsaro a Mali, lamarin da ya jefa kasar cikin yanayi na juyayi. Hukumomi sun bayyana kwanaki na zaman makoki.

https://p.dw.com/p/4FP79
Soldaten in Mali
Hoto: Florent Vergnes/AFP/Getty Images

Hukumomi a Mali, sun ayyana kwanaki uku a matsayin na zaman makoki a fadin kasar sakamakon wasu hare-hare biyu da mayakan tarzomar suka kaddamar a kasar a karshen makon da ya gabata.

Hare-hare ne dai da suka yi sanadiyyar salwantar sojoji da jami'an 'yan sanda a kasar da ke yankin yammacin Afirka.

Mahukunta sun ce hari da mayakan na tarzoma suka kai yankin Gao da ke arewacin Mali, ya salwantar da sojoji 42 ne cikin alkaluma na baya-bayan nan.

An dai yi zargin mayakan na IS da amfani da jirage marasa matuka da wasu manyan makamai irin na artillery.

Haka nan ma daga kudancin Malin iyaka da Burkina Faso, jami'an 'yan sanda biyar suka gamu da ajalinsu wasu kuma uku suka bata, danyen aikin kuma da tuni kungiyar JNIM mai mai alaka da al-Qaeda ta dauki alhakin kisan 'yan sandan.