1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali na ci gaba da neman dunke baraka

July 29, 2020

A ci gaba da kokarin yayyafa wa rikicin Mali ruwa, cikin sa'o'in da suka gabata Firaminista Boubou Cisse, ya ziyarci jigon mai adawa da gwamnati, wato Mahmoud Dicko.

https://p.dw.com/p/3g63I
Premierminister von Mali Boubou Cisse
Hoto: Pressedienst d. Premierministers von Mali

Firaministan na kasar Mali Boubou Cisse, ya bukaci Imam Mahmoud Dicko, wanda a hannu guda babban malami ne mai wa'azin addinin Islama da kuma ke da karfin fadi a ji, da ya karbi tayin sasanci da gwamnati ta bayar, musamman ma wajen shawo kan jiga-jigan masu zafin adawa da gwamnatin.

A ranar Litinin da ta gabata, kungiyar ECOWAS ta bukaci Shugaba Ibarhim Boubacar Keita da ya samar da gwamnatin hadaka, sannan ya yi gyara ga kura-kuran siyasa ta suka haddasa husumar da kasar ta fada.

Sai dai a nasu bangaren masu adawa da gwamnatin na Mali, sun yi watsi ne da shawarar ta ECOWAS, wadda wasu shugabannin Afirka ta Yamma suka bayar a zama karo na biyu da suka yi a Bamako abban birnin kasar.