1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bamako: 'Yan adawa da masu mulki sun tattauna

Salissou Boukari MNA
June 8, 2018

Manyan jam'iyyun da ke mulki a Mali sun yi wani zama tare da bangaren 'yan adawa a wani mataki na fahimtar juna don kaucewa wani sabon tashin hankali bayan wanda aka fuskanta na ranar biyu ga watan Yuni.

https://p.dw.com/p/2zAOQ
Ibrahim Boubacar Keita Präsidentschaftskandidat in Mali
Hoto: Reuters/Adama Diarra

Yayin wannan zaman taro da ke zuwa kasa da watannin biyu kafin zaben shugaban kasar ta Mali, Firaministan Soumeylou Boubeye Maïga, ya sha alwashin ci gaba da tuntubar 'yan adawa da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an gunadar da zabukan kasar cikin kyakkyawan yanayi da amincewar kowa.

Yayin da Firaministan ya ce tattaunawar ta su da 'yan adawa ta gudana cikin kyakkyawan yanayi, a hannu daya kuma Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai, da kuma Amirka, nuna fargabarsu suka yi dangane da tashe-tashen hankulan da aka fuskanta tsakanin bangarori biyu na 'yan siyasar kasar Mali a ranar biyu ga watan Yuni.