1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malawi ta fara kulle don yaki da corona

Mouhamadou Awal Balarabe
August 9, 2020

kasar Malawi ta rufe wuraren ibada da wuraren shan barasa sakamakon fargabar yaduwar cutar coronavirus a cikin kasar. Tun a watan Afirilu ne ta so sanya dokar kulle amma kotu ta ja mata birki a wancan lokaci.

https://p.dw.com/p/3ggw3
Gottesdienst
Hoto: CC/khym54

Gwamnatin Malawi ta ba da umurnin rufe wuraren shan barasa da majami'u tare da sanya dokar amfani da kyallen rufe baki da hanci don hana yaduwar cutar sarkafewar numfashi ta corona. Wannan matakin da ya samu amincewar kotu ya zo ne watanni uku bayan da wani alkali ya hana gwamnati sanya dokar kulle sakamakon rashin daukar matakan kare marasa karfi na kasar. Tun lokacin da annobar ta bulla a kasar a watan Afrilu, wadanda suka kamu  corona suka ninka sau biyu musamman a cikin makonni hudun da suka gabata.

Daga wannan rana ta Lahadi, ba a yarda da taron mutane sama da 10 a fadin kasar ta Malawi ba, yayin da jana’iza kuma ba za ta zarta samun mutane sama da 50 ba. Babban mai shigar da kara na wannan kasa Chikosa Silungwe ya ce za a yi amfani da jami'an tsaro don tabbatar da cewa jama'a sun mutunta matakan yaki da corona sakamakon fargabar da ake yi na yaduwarta a cikin kasar.