1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malawi: Rikicin siyasa ya koma kotu

March 26, 2020

Rahotanni daga kasar Malawi na cewa Mataimakin Shugaban Kasa Sailos Chilima ya kai Shugaba Peter Mutharika kara a gaban wata kotu a kasar.

https://p.dw.com/p/3a4tE
Schottland | Präsident von Malawi Peter Mutharika zu Besuch in Edinburgh
Hoto: picture-alliance/dpa/empics/PA Wire/Scottish Daily/F. Bremner

Chilima yana zargin mai gidansa Shugaba Mutharika da gaza sauke kwamishinonin zabe na kasar wadanda suka yi aikin zabe a babban zaben kasar na shekarar da ya gabata. 

A watan Fabrairun da ya gabata ne dai kotun tsarin mulkin kasar ta sanar da soke nasarar da Shugaba Mutharika ya samu zaben watan Mayu na 2019. Kotun ta ce ta gano cewa an tabka abubuwan da ba su dace ba a yayin zaben.

A cikin takardar shigar da kara da mataimakin shugaban kasar ya rubuta ya ce akwai wani kwamiti na 'yan majalisa da ya gano cewa wadannan kwamishinoni da Shugaba Mutharika yaki cirewa, ba su dace da gudanar da sabon zaben da ake shirin gudunarwa a ranar 2 ga watan Yuli a  kasar ba. Sai dai ana nuna zullumin ko zaben zai gudana domin Shugaba Mutharika ya daukaka kara a kan soke zaben da aka yi masa.