1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Succès Masra a siyasar kasar Chadi

Abdourahamane Hassane
May 18, 2026

Mene ne makomar jam'iyyar Les Transformateur ta tsohon firaministan Chadi Succès Masra da magoya bayansa bayan yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari?

https://p.dw.com/p/5Dv9Y
Tsohon firaministan Chadi Succès Masra a lokacin wani taron siyasa
Hoto: Joris Bolomey/AFP

Ana tsare da tsohon firaministan ne a gidan yari a kan hukuncin daurin shekaru 20, saboda samunsa da laifin tunzura al'umma, bayan wani tashin hankali na ƙabilu a kudancin Chadin.Tun bayan kame jagoran ‘yan adawar Succes Masara jam'iyyarsa ta Tansformateur ta ke fadi tashin gani an sake shi. Dr Tog-Yeum Nagorngar shi ne sakataran jam'iyyar.

Chadi: Ko kame madugun adawa na da tasiri?

Jamiyyarmu tana nan kalau ta kuma ci gaba da samun karbuwa duk da cewa shugabanmu Succès Masra, ba ya nan, an daure shi a kurkuku kan karya. Bugu da ƙari, jam'iyyar tana bunƙasa kuma tana mayar da hankali kan manufofinta, ba tare da wani tsoro ba. Dr. Succès Masra bai yi wani abu da ya sa aka daure shi ba a cikin shekarar da ta gabata. Babu wata ƙaramar shaida da aka gabatar don tabbatar da zarge-zargen da ake yi masa. Mun tabbata cewa wannan kuskure ne na hukumomin gudanarwa. Kuma mutum ɗaya tilo ke da dukkan ikon da ake buƙata don gyara wannan kuskuren shine Marshal Mahamat Idriss Déby Itno. Muna fatan zai ɗauki alhakin.

Koma-baya ko ci-gaba a siyasar Chadi?

Hoton birnin N'Djamena na kasar Chadi
Hoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

Kasar Chadi dai tana cikin wani hali na kara tsaurara wa 'yan adawa. A makon da ya gabata, an kama wasu shugabannin jam'iyyun adawa guda  takwas, mambobin kungiyar tuntuba ta 'yan siyasa (GCAP).

 Wadanda aka kama saboda shirin gudanar da zanga-zangar lumana, wadanda aka yanke musu hukuncin daurin shekaru takwas a gidan yari saboda an yi musu zargin laifukan, tayar da zaune tsaye da mallakar makamai ba tare da izini ba. Sosthène Mbernodji, shi ne shugaban kungiyar MCPL mai fafutika.

Jami'an tsaro sun kama jagoran adawan kasar Chadi

Jagoran adawa Succès Masra da shugaba Mahamat Idriss Deby Itno
Hoto: ISSOUF SANOGO/DENIS SASSOU GUEIPEUR/AFP/Getty Images

"Tun lokacin da aka daure shugaban jamiyyar transformateur shekara guda da ta gabata, an rage musu hanzari. Sannan ƙungiyar tuntuba ta 'yan siyasa (GCAP) ita ce kaɗai ƙungiyar da ta rage, tana ba da ra'ayin suka. Yanzu, gwamnati ta yi amfani da kotuna don wargaza wannan ƙungiya ta kuma rufe shugabanninta takwas. Ina ganin ba ma cikin dimokuraɗiyya muna cikin mulkin mallaka wanda ke ƙara yin ƙarfi, kuma wannan abin baƙin ciki ne ga Chadi. Ina ganin lokaci ya yi da za a rage rikicin zamantakewa da siyasa domin ci gaba. Domin a wannan matakin, mun koma baya da kusan shekaru 40 zuwa 50. Ƙasar ta koma tsarin jam'iyya ɗaya, kamar a zamanin 'yancin kai."

Dangane da wannan kame-kame na 'yan siyasar da ake yi a Chadi, wasu jam'iyyun adawa guda 20 sun yi Allah wadai a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar kan rufe bakin 'yan adawa da nuna rashin adalci wajen gudanar da mulki.Jami'an tsaro sun kama jagoran adawan kasar Chadi