1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Siriya na cikin rudani

November 1, 2013

Rikicin da ake ciki a kasar Siriya na kara sukurkucewa ta bangaren soji.

https://p.dw.com/p/1AAMr
Hoto: picture-alliance/dpa

Rikicin da ake ciki a kasar Siriya na kara sukurkucewa, yayin da ake shirin gudanar da taro kan shawo kan abin da ke faruwa.

Rikicin kasar ta Siriya ya zama wani abin da babu wanda ya yi nasara a kai. Tun lokacin gwamnati da kungiyar Hisbollah da suke alaka, suka kwace garin al-Kusair cikin watan Yuni, har kawo yanzu babu wata nasarar kirki da suka sake samu. 'Yan tawaye sun rike garin Deraa na kudanci, sannan wasu kungiyoyi na rike da wasu kananan wurare.

Joshi Shashank masanin harkokin tsaro a wata cibiya ta kasar Birtaniya, ya nuna irin wannan hali da ake ciki na rashin tabbas:

"Ina tsammani abin da muke gani shi ne, yadda ko wani bangare ke karfafa matsayi a inda yake a sassa daban-daban na kasar na neman fadada wuraren da ke hannun ko wani sashi."

Wannan rikici na kasar Siriya ya yi awun gaba da dubban daruruwan rayuka. Amma yanzu duk sassan da ke rikici babu wani da ya samu wata nasarar kirki, illa ci gaba da rarraba kasar.

Syrische Flüchtlinge in Bulgarien
Hoto: picture-alliance/dpa/Vassil Donev

Eyal Zisser masanin kan lamuran kasar Siriya a Jami'ar birnin Tel Aviv yana mai ra'ayin cewa:

"Lissafin gwamnatin shi ne, a hankali 'yan tawayen za su gaza."

Shugaban kasar ta Siriya Bashar al-Assad na karfafa matsayin da yake, tun tsakiyar shekara 2012. Kuma ga alamu mafi yawan kasashe da ke da hannu a rikicin basa bukatar faduwar gwamnati. Tun lokacin da gwamnatin Siriya ta ba da hadin kai wa jami'in hukumar lalata makamai masu guba, take samun karbuwa tsakanin kasashen duniya.

Muddun gwamnati ta ci gaba da ba da hadin kai wa jami'an da ke lalata makaman, gwamnatin za ta kawar tunanin yuwuwar samun wani hari daga kasar Amirka. Kuma gwamnati za ta iya gabatar da matsaya guda lokacin taron da za a gudanar nan gaba cikin wannan wata na Nowamba. Yayin da 'yan tawaye ke ci gaba da zama a rarrabe, da kara samu masu tsananin kishin Islama, abin da ya janyo kasashen Yammaci Duniya ke dari-dari da 'yan tawaye.

Albert Stahel yana zama farfesa a jami'ar birnin Zurich na kasar Switzerland, ya ce gwamnatin Assad tana da sauran sauran tasiri:

FILE - In this Wednesday, Aug. 28, 2013 citizen journalism image provided by the United media office of Arbeen which has been authenticated based on its contents and other AP reporting, members of the UN investigation team take samples from sand near a part of a missile that is likely to be one of the chemical rockets according to activists, in the Damascus countryside of Ain Terma, Syria. Russia's proposal to place Syria's chemical weapons stockpile under international control for dismantling would involve a lengthy and complicated operation made more difficult by a deep lack of trust. Syria is believed by experts to have 1,000 tons of chemical warfare agents scattered over several dozen sites across the country, and just getting them transferred while fighting rages presents a logistical and security nightmare. (AP Photo/United media office of Arbeen)
Hoto: picture alliance/AP Photo

"Babu wanda yake bukatar faduwar gwamnatin"

Ya ce kasashen Turkiya da Saudiyya ne kawai ke neman ganin faduwa gwamnatin Assad. Amma duk sauran ko suna adawa da kasancewar Assad basa goyon bayan faduwar gwamnatin.

Ya kara da cewa gwamnatin birnin Damusuks ta zama wadda ke dai-dai ta lamaru. Kuma kasashen Amirka, da Rasha, da kuma Iran duk babu mai bukatar faduwar gwamnati. Gamayyar 'yan adawa masu sassaucin ra'ayi za su gabatar da matsayi nan gaba kadan bisa yuwuwar halartar taron shawo kan rikicin kasar, ko kuma kauracewa. Wannan yayin da kasar ke ci gaba da sukurkucewa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman