Makokin 'yan yawon buɗe daga Hong Kong
August 26, 2010A Hong Kong, an yi zaman makokin wasu 'yan wannan jiha su 8 da suka gamu da ajalinsu a ƙasar Filipins bayan da wani tsohon ɗan sanda ya yi garkuwar da su bisa buƙatar mai da shi bakin aikinshi. Kimamin mutane ɗari biyar ne dai suka halarci wannan zaman da gwamnan wannan yanki, Donald Tsang ya jagoranta a dandalin Bauhinia. Sai da aka yi kawaici na minti uku tare da sassauta tutoci domin tunawa da marigayan da suka gamu da ajalinsu da yammacin Litinin da ta gabata. 'Yan yawon buɗe ido guda 8 ne suka mutu wasu kuma su 7 ne suka samu raunuka bayan da Ronaldo Del Rosario tsohon ɗan sandan ƙasar ta Philippines ya shafe awa goma yana garkuwa da su bisa buƙatar mai da shi bakin aikinshi. Daga cikin waɗanda suka halarci zaman makokin har da biyar da suka tsira da rayukansu da kuma jami'an gwamnati. Da yammacin jiya Laraba ne aka ɗauki gawawwakin zuwa Hong Kong.
Mwallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu