Makokin tunawa da harbo jirgin Malesiya | Labarai | DW | 17.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makokin tunawa da harbo jirgin Malesiya

A kasar Ukraine a wannan Litinin ce dangi da 'yan uwa da aminnan arzikin mutanen da suka mutu a cikin jirgin saman Malaisian Airlines da aka harbo da makami mai lizzami a gabashin kasar lokacin yaki ke zaman makoki.

A lokacin wannan taron makoki wanda zai gudana a wannan Litinin a karkashin jagorancin sarki William Alexander da Sarauniya Maxima na masarautar Hollande, Mutane kimanin 2000 daga cikin dangin mamatan za su yi zobe a wani shingen itatuwa 298 da aka shuka a wurin da jirgin ya fado a matsayin shaidar nuna alhini ga mutanen 298 da suka rasu a lokacin faduwar jirgin. 

A ranar 17 ga watan Yulin shekara ta 2014 ne dai a tsakiyar yakin kasar Ukraine wani makami mai lizzami kirar kasar Rasha ya kakkabo  jirgin na Malesiya Airlines dauke da fasinjoji 298 da suka hada da 'yan kasar Hollande 196.