Majalisar Tarayyar Turai ta soki Isra′ila | Labarai | DW | 19.04.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Tarayyar Turai ta soki Isra'ila

Majalisar Tarayyar Turai ta yi kiran Isra'ila da ta daina duk wani amfani da karfi kan Falasdinawa masu zanga-zanga a kan a iyakar Zirin Gaza da Isra'ila.

Hakan ya biyo bayan dauki ba dadin da ake yi tsaranin bangarorin a iyakar Zirin Gaza da Isra'ila wanda ya haddasa mutuwar mutane sama da 30 a bangaran Falesdiwa. Cikin kudiri da majalisar ta Tarayyar Turai ta dauka wanda ya samu babban rinjaye 'yan majalisar sun yi Allah wadai da matakan da Isra'ilan ke dauka wadanda suka haddasa mutuwar Falesdinawa da basu ji basu gani ba tare da jikkata wasu a yankin Zirin na Gaza 'yan makonni uku na baya-bayan nan. Iyakar ta Isra'ila da yankin Zirin Gaza na Falesdinu ta kasance cikin tashin hankali tun daga ranar 30 watan Maris da ya gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 34 da kuma wasu daruruwa da suka samu raunuka ta hanyar harbinsu da aka yi da harsasai na gaskiya.