Majalisar Faransa ta tsawaita dokar ta baci | Labarai | DW | 19.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Faransa ta tsawaita dokar ta baci

Majalissar dokokin Faransa ta amince da matakin tsawaita dokar ta baci da wata uku a duk fadin kasar wacce ta kuma tanadi wasu sabbin matakai na zamani na yaki da ta'addanci

Majalisar dokokin Faransa ta amince da matakin tsawaita dokar ta baci da tsawon watanni uku a duk fadin kasar lokacin wata mahawara da ta shirya a wannan Alhamis.Dokar wacce gwamnati ta shigar a gaban majalisar dokokin biyo bayan harin birnin Paris ta tanadi wasu sabbin matakan yaki da ta'addanci na zamani da za bai wa kasar damar kalubalantar barazanar da kungiyoyin 'yan ta'ada ke yi ga zaman lafiyar kasar ta Faransa .

Da ya ke jawabi a gaban majalissar dokokin kasar a yau Firaministan kasar ta Faransa Manuel Valls ya ce akwai ma yiwuwar Faransar ta fuskanci harin makamai masu guba a nan gaba.