Majalisar dokokin Najeriya ta yi kwanaki 100 | Siyasa | DW | 17.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Majalisar dokokin Najeriya ta yi kwanaki 100

A Najeriya a ranar Alhamis ne aka cika kwanaki 100 da kafa majalisar dokokin kasar. Ko yaya ake kallon aiyyukan da ta yi a wadannan kwanaki har da majalisar fuskantar suka?

A Najeriya a ranar Alhamis ne aka cika kwanaki 100 da kafa majalisar dokokin kasar ta 8, wacce ta fuskanci rigingimu na shugabanci tun farkon kafuwarta, abinda ya haifar da yawan dage zaman majalisar. Ko yaya ake kallon aiyyukan da ta yi a wadannan kwanaki da ya sanya majalisar fuskantar suka?

Tun dai farko da takadamma na zaben shugabaninsu da ta kaisu ga damben kutufo wajen zaben sauran shugabanin, musamman a majalisar wakilan Najeriyar, abinda ya sanya haifar da yawan dage zaman majalisar sau da dama a cikin watannin farko na fara zamansu.

Wannan ya haifar da samun bangarori biyu a majalisar wakilan da ta dattawan Najeriya, abinda kai tsaye ya shafi kwanakinsu na farko day a kamata a ce sun yi nisa wajen aikin na kafa dokoki da sanya idannu. A cikin kwanaki 100 na kafa majalisa ta 8 da ta zo da zumar samar da canji na gwamnati karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ko ya ake kallon zaman da suka yi, bisa la'akari da makudan kudaden albashi da alawus da suka karba ke tsole idanun ‘yan Najeriya? Mallam Awal Musa Rafsanjani shine shugaban kungiyar Cisilac da ke sa ido a aiyyukan ‘yan majalisu a kasar.

‘'Wannan majalisda ta 8 a gaskiya ta zo da mishkiloli da dama iya adadin kwanakin da ake zaton za su iya zaunawa su yi aiki don taimakawa kasa basu yi wannan zaman ba, sannan babu wani gagarumin batun da aka yi, ko sanya idannu a kan dokoki da aiyyukan gwamnati. Kuma babu wani ciakken zama da aka yi don zaman tattauna matsalolin Najeriya, abinda ke bamu tsoro kenan''

Koda yake bayan kwanaki 100 da kafuwar majalisa ta takwas din har yanzu bata kaiga kafa kwamitocinta bad a ake gani sune ya kamata su zaburara da aikin majalisar, amma ga Ho Abdulrazaq Sa'ad Namdas yace sun yi aiki tukuru a cikin wadannan kwanaki daya kamata a jinjina masu.

"Cikin kwanaki 100 nan mu a majalisar tarayya mun gabatar da kudurori kusan 77, a cikinsu mun yi aiki a kan 35, kuma mun yi kudurorin doka watau bill guda 39 wadanda aka yi masu karatu na farko. Don mun sanar da shugaban kasa cewa a kafa dokar ta baci a fannin bada aiki da samarwa mutane aiki, mun ma ce a bincika mana me yasa kasashen Turai suka hana a kai kayan abincinmu irin su wake zuwa kasashensu. Mun bincika, mun gano cewa ashe tuni da dadewa sau hamsin suna sanar da gwamnati amma ba a dauki mataki ba. Mun taba abubuwa masu muhimmanci, wanda gaskiya ya kamata mutane su yaba mana''

Yawan dage zaman majalisa da a lokutan baya kan kawo cikas ga aikin majalisun dokokin Najeriya, inda sukan karasa da hamzarin amincewa da dokoki kafin kamalla zamansu, koma gaza kamalla muhawara a kudurori masu muhimmanci irin na kudurin sake fasalin harkar man Najeriya da aka kwashe shekaru da dama ana muhawara a kansa na zama abin daga hankali. Ga Awal Musa Rafsanjani na ganin lokaci fa ya yi da zasu canza don hatsarin da ke tattare da jan kafar da suke yi da aikinsu.

A yayinda ake sa idon dawowar majalisar a ranar 29 ga watan nan bayan shan hutu na holewa na tsawon makwanni shida, a dai-dai lokacin da shugaban Najeriya ke shirin aikewa da sunayen mutanen da zai nadaministoci ga ‘yan majalisar don tanatance su, za a sa ido don ganin ko salon canjin da shugaba Buhari ke kokarin aiwatarwa ya bulla a kuryar majalisar.

Sauti da bidiyo akan labarin