1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya za ta tura tawagar bincike el-Fasher

Binta Aliyu Zurmi
November 15, 2025

Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tura tawagar bincike mai zaman kanta zuwa birnin el-Fasher na kasar Sudan.

https://p.dw.com/p/53fb1
UNO Menschenrechtsrat Genf 2025 | Volker Türk bei Sondersitzung zur Menschenrechtslage in und um El Fasher
Hoto: Salvatore Di Nolfi/KEYSTONE/picture alliance

Matakin dai ya biyo bayan ta'asar cin zarafin fararen hula da aka ruwaito sojojin da ke rikici da sojojin Sudan sun tafka.

Shugaban hukumar Kare Hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya ce laifukan da aka aikata a kwanakin baya-bayan nan a el-Fasher sun munana matuka.

Ya kuma yi gargadin karuwar tashe-tashen hankula a yankin Kordofan da ke tsakiyar kasar Sudan, wanda tuni wasu rahotanni ke bayyana kazantar lamura a yankin.

Yankin Kordofan dai ya kunshi jihohi uku kuma ya kasance matsuguni a tsakanin yankunan yammacin Darfur na karkashin ikon dakarun RSF da kuma jihohin da ke hannun sojoji a yankin gabashin kasar.

 

Karin Bayani: Dakarun RSF a Sudan amince da kudurin sulhu