Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci dage zabe a Burundi | Labarai | DW | 26.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci dage zabe a Burundi

A ranar Litininin ne dai aka tsara cewa za a yi zaben 'yan majalisar dokoki sannan a yi zaben shugaban kasa a ranar 15 ga watan Yuli.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'an nan ya bukaci mahukunta a kasar Burundi su gaggauta yin duba ga shirin dage zaben kasar duba da halin da demokradiyar kasar ta samu kanta ga rashin tsaro.

Sakatare Ban Ki-moon ya mara baya ga kiraye-kirayen kasashen yamma da na Afirka wadanda su ka bukaci a dage zaben bayan da kasar ta shiga rudani bayan zanga-zangar adawa da shirin neman tazarcen shugaba Nkurinziza a karo na uku.

A ranar Litininin ne dai aka tsara cewa za a yi zaben 'yan majalisar dokoki sannan a yi zaben shugaban kasa a ranar 15 ga watan Yuli. Zaben da 'yan adawa su ka ce za su kaurace masa.