Majalisar Birtaniya tana tattauna shirin kadsdamar da farmaki a Siriya | Labarai | DW | 02.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Birtaniya tana tattauna shirin kadsdamar da farmaki a Siriya

Majalisar dokokin Birtaniya tana mahawara mai zafi kan shirin neman kaddamar da farmaki kan tsagerun kungiyar IS a Siriya.

Majalisar dokokin Birtaniya tana tattaunawa a wannan Laraba kan shirin shiga kai hare-hare sansanonin tsagerun kungiyar IS da ke cikin kasar Siriya. Firaminista David Cameron ya kara kaimi kan shirin tun bayan hare-haren da aka kai birnin Paris na kasar Faransa da kimanin mutane 130 suka hallaka cikin watan jiya na Nuwamba.

Majalisar dokokin za ta shafe sa'oi tana tattauna duba yuwuwar kaddamar da hare-haren. Shugaban marasa rinjaye na majalisar Jeremy Corbyn kana shugaban jam'iyyar adawa ta Labour ya bukaci kar a yi gaggawa wajen shiga yakin. Ana fafata mahawara mai zafi a majalisar dokokin ta Birtaniya kan wannan shiri.