1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisa ta amince da gyaran kudin tsarin mulki

July 25, 2013

A yanayin da ke nuna fatan samun sauyi a tsarin mulkin Najeriya, majalisar wakilai ta amince da muhimman sauye-sauye a aikin gyaran fuska ga tsarin mulkin kasar tare da baiwa kananan hukumomi yancin cin gashin kansu

https://p.dw.com/p/19EP8
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

To sun dai kwashe daukacin ranar Laraba har zuwa talatainin dare a kan wanan aiki inda bayan da suka jefa kuri'ar suka kasa kuma suka tsare domin kaucewa coge dama magudi a kan kuri'ar da suka jefa domin sauya tsarin mulkin Najeriyar. Sun dai amince da cire kariyar fuskantar shari'a ga shugaban kasa da gwamnoni da ikon dan takara mai zaman kasa a matakin tarayya da jihohi, da kuma batun duk inda aka haifeka ka tashi to ka zama dan kasa a wannan wurin. Daya bayan daya dai shugaban majalisar wakilai Hon Aminu Waziri Tambuwal ya rinka karanto sakamkon kuri'ar da suka jefa kamar haka.

Abinda yafi daukan hankalin yan Najeriya shine amincewar day an majalisar suka yin a yin gyara ga dokar da zata baiwa kanan hukumomi ikon cin gashin kansu. Hon Abdulrazaq Nuhu Zaki yace sun yi hakan ne don biyan bukatun yan Najeriya musamman ma dai talakawa da suke wakilta a majalisar.

“Yace Kaman maganar batun yan sanda a jihohi da aka kawo wanda muka ki shi muka ce ya zama yadda yake a yanzu akwai kuma magnara zabe a kananan hukumomi ya zama a karkashin hukumar zabe ta kasa Inec wanda ita zata gudanar da zaben. Muna fata jihohi zasu bada goyon baya a wanan aiki''

Murna da farin ciki game da yadda zaben ya gudana ya sanya yan majalisar da ma sauran yan Najeriya da suka raba dare a zauren majalisar yin shewa da ma tafi a kan amincewa da sauye-sauyen. To shin menene gaskiyar zargin cewa wasu gwamnoni sun yi kokarin baiwa yan majalisar na goro domin kaucewa baiwa kananan hukumomi yancin cin gashin kansu da ma sauran batutuwa da yadda lamarin zai kasance dai dai da biyan bukatunsu. Hon. Ahmed Baba Kaita ya bayyana yadda lamarin ya kasance.

“Ba ko wai an kira wasu yan majalisa su je otel amma yan majalisa sun ce basu zuwa, wadansu kuma sun aiko sun ce a je a yi suna ganin suna da karfi kan yan majalisar su. Duk irin wadanan abubuwan kaga suna da nasaba da rayuwa kuma duk kasar da take son ta ci gaba sai ta samu daidaito a kansu kana ta yi tunanen ci gaba, irin batun kariyar nan ga shugabani mutum ya yi maka zilla ya sace milyoyin kudi a rasa yadda za'a yi da shi''.

Babu shakka maganar gyara a kan tsaroin mulkin Najeriyar da majalisar wakilan ta yi wanda ya sabawa wanda majalisar datawan kasar ta aiwatar ba zai yiwa masu rike da madafan iko dadi ba abinda za'a ja daga a matakan jihohi kafin a samu amincewa dasu.

DW_Nigeria_Integration-online6
Aso Rock: alamar hadin kan NajeriyaHoto: Katrin Gänsler

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Umaru Aliyu