1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Mai sarrafa tsirrai zuwa ganyen shayi

Maawiyya Abubakar Sadiq MAB
March 2, 2022

Usman Ibrahim Shehu da ya kammala digirinsa a Sokoto ya rungumi sana’ar sarrafa nau’ukan itatuwa zuwa ganyen shayi a wani mataki na dogaro da kai da kauce wa zaman jiran aikin gwamnati.

https://p.dw.com/p/47pSB
traditionelle Äthiopische Kaffeekanne und Tasse
Shan shayi na daya daga cikin al'adun 'yan Habasha da wasu kasashen AfirkaHoto: DW/A. Tadesse Hahn

Matashi Usman Ibrahim Shehu ya shafe sama da shekara guda yana gudanar da wannan kasuwanci na sarrafa nau'ukan tsirran itatuwa zuwa ganyen shayi. Ya ce  ‘'Akwai abubuwan da suke da amfani ga jikinmu, amma ba a san yadda za a sarrafa su ba ta yadda mutane za su amfana. Tun ina Jami'a nake bincike sosai  akan su muhimmancin wadannan ‘ya'yan itace da muke da su da kuma yadda muka sarrafa su. Shi ya ja hankalina na fara sarrafa wadannan abubuwa ta hanyar ganyen shayi da sauran su''.


Matashin ya samar da gurabun ayyukkan yi da dama a kamfaninsa. baya ga haka ya ce: "Kwastomomin da muke bai wa wannan ganyen shayi suna amafana da shi, kuma inda muke tunanin ganyen shayinmu bai kai ba, duk ya kai''.

A fannin matsaloli kuwa ya ce " 'Babban kalubalen da muke fuskanta shi ne yawan kwastomomin da muke da, sannan ba mu da manyan injunan da zamu sarrafa su, muna daukar lokaci, amma ba maiya sarrafa su da yawa domin mu gamsar da kwasstomominmu''.

Matashi Usman na mai cike da buri da kuma fatan samun manyan injiua da za su inganta wannan sana'a ta sarrafa nau'ukan tsirrai zuwa ganyen shayi.