Mai a Angola: tsakanin arziki da talauci | Man fetir a Angola | DW | 11.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Man fetir a Angola

Mai a Angola: tsakanin arziki da talauci

Kasar Angola ta mallaki dimbin arzikin karkashin kasa ciki kuwa har da man fetur, amma kuma al'umarta na ci gaba da rayuwa hannu baka hannu kwarya.

A karshen shekarun 1960 ne aka gano cewa arzikin man fetur na shunfude a karkashin kasar Angola. Amma dai ba ta fara hakoshi ba, sai bayan da ta kawo karshen yakin basasa na shekaru 27 da ta yi fama da shi. Angola ce kasa ta biyu da ta fi arzikin man fetur a nahiyar Afirka baya ga Tarayyar Najeriya.

Dinbim arzikin gas a karkashin kasa

Titel: Erdgasabfackelung in Angola Beschreibung: In Soyo, an der nördlichen angolanischen Grenze mit der Demokratischen Republik Kongo, spucken zwei horizontal verlegte Röhren eine meterhohe Feuerzunge in den Himmel. Das bei der Erdölförderung entstandene Gas wird in Soyo abgefackelt – noch funktioniert die erste LNG-Anlage des Landes in Soyo nicht, um das Erdgas zu verarbeiten. Copyright: Renate Krieger/DW Datum: 07.11.2012

Gurbata yanayi: kona gas mai guba a Soyo

Sannan kuma ta na da arzikin iskar gaz da ya kai kubik meta miliyan dubu 366 da ke shunfude a karkashin kasarta. Tun ma dai shekaru biyar da suka gabata ne dai ta fara kafa cibiyar da za ta hako wannan arziki na gas tare da tace shi. Girman wannan cibiya ya kai na filayen kwallon kafa guda 240. Sannan kuma kanfanin hako mai na Chevron ne ya mallaki akasarin hannayen jarin kanfanin, wanda ya fara hako Tonne miliyon biyar da dubu 200 na gaz a kowace shekara. Wannan kasa dai za ta kasance daya daga cikin kasashen Afirka da za su rika sayar da iskar gas a kasuwannin duniya.

Rashin aikin yi ga 'yan kasa

Titel: Erdgas Förderung Angola Beschreibung: Die erste LNG-Anlage Angolas ist noch nicht in Betrieb – dies sollte eigentlich Anfang 2012 geschehen. Die Anlage hat eine jährliche Produktionskapazität von 5,2 Millionen Tonnen Flüssigerdgas. Offiziell heißt es, die Anlage sei noch in der Testphase. Haupteigner der LNG-Anlage in Soyo, im Norden des Landes, ist die nordamerikanische Firma Chevron (36,4 Prozent Beteiligung). Angolas staatliche Firma Sonagás hat einen Anteil von 22,8 Prozent, die italienische ENI, die britische BP und die französische Total haben jeweils 13,6 Prozent. USA sind auch Hauptabnehmer des angolanischen Erdöls. Copyright: Renate Krieger/DW Datum: 07.11.2012 Copyright: Renate Krieger/DW Datum: 07.11.2012

Shiga harkar hako gas: Bututun gas a Soyo

Sai dai kuma duk da wannan arziki, kimanin kashi 40% na al'umar Angola na samun kasa da dala daya ta Amurka a rana a matsayin kudin shiga. Kana daidai da a garin Soyo inda aka kafa cibiyar hako iskar gas, ba a samun wadatar hasken wutar lantarki. lamarin da ke ci wa Luciano Nzombo Madia mai shekaru 32 a duniya tuwo a kwarya.

"Ba ka iya ganin tafin hannun ka da zarar dare ya yi a wannan gari saboda duhun da ke lullube shi. Wannan abin kunya ne. Mutun ba ya ganin komai a lokacin da ya ke tsallake hanya, alhali birnin ne da ke da dimbin arzikin karkashin kasa. Maimakon ya ci wannan gajiya, dada afkawa ya ke yi cikin talauci."

Titel: Angola Rohstoffe Schlagwörter: Luciano Madia Angola LNG Projekt Erdöl Förderung Erdgas Soyo Afrika Rohstoff Armut Reichtum Beschreibung: Der Taxifahrer Luciano Nzombo Madia war einst im Angola-LNG-Projekt beschäftigt, als Vorarbeiter bei der Verlegung der Pipelines für das LNG-Projekt. Nacht ist die Stadt ganz dunkel. Man sieht nicht einmal, ob jemand die Straße überquert. Und dabei ist die Stadt voller Erdöl. Statt Reichtum bringt das Armut. Copyright: Renate Krieger/DW Datum: 07.11.2012

Rashin amfana da arzikin kasa: Luciano Nzombo Madia direban tasi

Shi dai Luciano dake zama direban tasi, ya na cike da fatan ganin birnin Soyo da ma dai Angola ita kanta ta dogara kan arzikin da Allah ya hora mata wajen samar da ababen more rayuwa. Sai dai sabanin haka hanyoyin garin na dada lalacewa. Sannan kuma shi ma da kansa ya rasa aikin yi tun bayan da aka kammala gina cibiyar hako iskar gaz a shekara ta 2011. A halin yanzu ya dogara kan aikin tasi wajen samun kimanin dalar Amurka 150 a kowace rana. Alhali albashinsa na baya ya ninka wannan adadi. Saboda haka ne ya ke nuna takaicinsa game da alkawuran samar da guraben aiki da 'yan siyasan Angola ke yi a lokacin yakin neman zabe ba tare da cikawa ba.

"Suna fada a ko da yaushe cewa idan Angola ta fara hako iskar gaz, to lallai kasar za ta habaka. Amma abin takaicin ,shi ne mutane kalilan ne suke cin gajiyar arzikin. A halin da ake ciki dai 'yan Angola da dama sun je cin rani a kasashen waje."

Luanda da arzikin man fetir

Titel: Luanda Hauptstadt Angola Avenida Marginal 4 de Fevereiro Beschreibung: Die neue Avenida Marginal in Luanda. Alle Ampeln funktionieren auf einer Strasse, wo im Vergleich zu anderen Vierteln der Hauptstadt Angolas sehr wenige Autos fahren. Die fünf-Millionen-Metropole zählt zu den teuersten Städten der Welt, die Miete eines Hauses kann im Zentrum bis zu 5.000 Dollar kosten. Eine Studie der Regierung sagt andererseits, 40% der Bevölkerung lebe mit weniger als einem Dollar pro Tag. Copyright: Renate Krieger/DW Datum: 05.11.2012

Gine ginen kasaita a unguwar Avenida Marginal dake birnin Luanda

A Luanda babban birnin Angola ne ake ganin duk wani abu na kasaita da kasar ta samu bayan fara hako man fetur. Birnin na daya daga cikin wuraren da suka fi tsadar rayuwa a duniya. Dakin haya na iya kai wa dollar 5000 na Amurka a kowane wata.

A daya hannun kuma kanfanonin da ke hako fetur da iskar gas sun gina sabbin ofisoshi da gidajensu na kwana. Yayin da saye sayen manyan motoci na kawa ke neman zamewa gasa a tsakaninsu. Kashi 98% na kudaden shigar gwamnati na fitowa ne daga cinikin man na fetur da kuma iskar. Sai dai a cewar Elias Issac, shugaban kungiyar kare hakkin bil Adama ta Open Society Angola, mutanen da suke amfana daga wannan arziki ba su taka kara sun karya ba.

"Alkaluma sun nunar da cewa kasa da kashi daya bisa 100 na al'umar Angola ne ke aiki a kanfanonin da ke hako arzikin na karkashin kasa. Mun samu makudan kudade da muka yi amfani da su wajen gine gine baya yakin basasa da kasar ta yi fama da shi. Tabbas abu ne da ya dace. Amma kuma ya zama ci gaban mai hakon rijiya domin al'uma na fama katsewar wutar lantzarki da kuma rashin tsaftaceccen ruwan sha."

epa03368880 José Eduardo dos Santos, MPLA candidate for president of Angola, talks to supporters during his political rally at on the Square of Independence, Luanda, Angola, 24 August 2012. Angola will hold general elections on August 31, which will define the composition of parliament and the names of the President and Vice President of the Republic. EPA/PAULO NOVAIS

Shugaban dos Santos a yakin neman zaben 2012

Kashi 35% na al'umar Angola na rayuwa cikin tsananin talauci a halin yanzu a cewar wani rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar. Sai dai a cewar rahoton shekaru 13 da suka gabata kashi 54% na 'yan Angola ne ba sa iya shigar da taro ko sisi a aljuhunsu a rana. An samu sararawar al'amura ne sakamakon bunkasar tattalin arziki da man fetur da kuma iskar gaz suka jawo wa Angola.

Jam'iya daya ke da karfin fada

Masanin harkokin shari'a kana mamba a jam'iyar MPLA da ke mulki wato Norberto Garcia ya baiyana wa Deutsche Welle cewa ba rabon tsabar kudi ne zai kyautata halin rayuwar al'uma ba. A'a, amma dai ba su horon da ya dace.

Was ist mit rund 32 Milliarden Dollar passiert, die die staatliche Erdölfirma Sonangol 2007 bis 2010 erwirtschaftet hat?, fragt sich der IWF. Elias Isaac von der Open Society erklärt: Es gibt heute zwar mehr Information über die Gelder, aber keineswegs mehr Transparenz. Korruption sei laut Kritikern in Angola kein Fremdwort: es heißt Gasosa (Sprudel). 07.11.2012, Luanda Copyright: DW/Renate Krieger

Kashi daya bisa hudu na yan Angola matalauta ne. Shin ina kudin man ke kwarara?

"Hanya mafi a'ala ta wadata al'uma da arziki ita ce ta samar da musu da guraben aiki. Wannan ba zai hana gwamnati aiwatar da manufofin da ta sa a gaba ba. sai dai kuma a angola, mutane ba su da horon da ya dace da aiyukan da ake da su. Kashi 34 daga cikin 100 ba su iya karatu da rabutu ba, lamarin da ke kawo cikas wajen samar musu da aiyukan da suka dace. Dole ne gwamnati ta nakaltar da al'uma makamar aiki, domin da shi za su dogara wajen samun aiki."

Ita dai gwamnatin ta Angola ta kaddamar da manufofin raya kasa da ta ke so ta cimma kan nan da shekar ta 2017 da nufin kyautata halin rayuwar talakawanta. Daga cikin aiyukan da ta sa a gaba har da wadata al'uma da ruwa mai tsafta da kuma wutar lantarki, da ma uwa uba rage radadin talauci da suke fama da shi.

Rashin hanyoyin mota masu kyau

Titel: Das Armenviertel Zango I in Viana, Angola Beschreibung: In Viana, einem Vorort von Luanda, warten von der Regierung vertriebene Bürger auf ein neues Zuhause. Sie wohnten in Luanda, wurden wegen dem Bau einer Straße weggeschickt. Im Viertel Zango bauten sie sich Blechhütten. Ganze Familien überleben mit knapp 300 Dollar im Monat. Copyright: Renate Krieger/DW Datum: 10.11.2012

Unguwar marasa galihu a Viana

A wata unguwa ta ya ku bayi mai suna Cazenga da ke birnin Luanda , tituna basu da kwalta. Sannan kuma wutar lantarki 'yan sa'o'i suke samuwa a rana a cewar Euricleurival Vasco, wani direba da ke yi wa gwamnai aiki.

"Mun shafe mako guda ba tare da wutar lantarki ba. Amma yau an kawo mana wuta. Sannan aka yanke daga baya. Injiniyan da ke aiki a hukumar wutar lantarki ya ce ba su samu mai da za su yi amfani da shi wajen tayar da janareto ba. ban sani ba ko ya kamata mu yarda da abin da ya fada ba."

Amma kuma a daya shiya na babban birnin na Angola, ana ci gaba da gina sabbin gidaje a unguwar Kilimba domin sayar wa al'uma a farashi mai rahusa. Sai dai ya zuwa yanzu gidaje 220 aka sayar cikin 3000 da aka gina. Wannan dai ya na daya daga cikin alkawuran da shugaba Eduardo dos Santos ya yi lokacin yakin nema zabe, na gina sabbin gidaje miliyan daya masu saukin kudi. Tattalin arzikin Angola ta samu bunkusar kashi bakwai daga cikin 100 na shekara ta 2012. Amma dai ta kai kashi 20 daga cikin a shekarun baya. Amma dai wadanda ke cin gajiya sune 'yan boko da 'yan kasuwa da ke dasawa da gwamnatin dos Santos.

Mawallafa: Renate Krieger / Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin