1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Rufe mahakar zinare a Maradi

November 10, 2021

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dauki aniyar rufe mahakar zinare ta garin Kwandago da ke karamar hukumar Dan Issa, sakamakon asarar rayuka da aka samu a mahakar.

https://p.dw.com/p/42ou1
Nigeria Bauchi Bergbau
A lokuta da dama, masu hakar zinare ba bisa ka'ida ba kan rasa rayukansuHoto: DW/Aliyu Muhammed Waziri

A cikin wani kudiri da ta dauka yayin taron majalisar ministoci na baya-baya nan, gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar ta bayyana matakin rufe mahakar. Mutane 18 ne dai suka rasa rayukansu, a yayin hadarin da ya faru sakamakon ruftawar wasu rijiyoy a mahakar zinaren. Cikin wadanda suka rasuan akwai 'yan Jamhuriyar ta Nijar Biyar da 'yan Najeriya 13. Tuni dai kungiyoyin farar hula suka fara fargaba, dangane da abubuwan da ka iya biyo bayan rufewar kamar karuwar zaman kashe wando saboda rashain aikin yi da fashi da makamai da sace-sace har ma da kila garkuwa da mutane. Acewar kungiyoyin akwai bukatar hukumomin su sake yin nazari kan wannan al'amari, domin ka da a bar baya da kura.