1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Mahawara kan taron birnin Pau

Salissou Boukari GAT
January 13, 2020

A Jamhuriyar Nijar, mahawara ce ta kaure tsakanin 'yan kasar a game da matakin Shugaba Mahamadou Issoufou na halartar taron tsaro na birnin Pau a Faransa a daidai lokacin da kasar ke zaman makokin mutuwar sojojinta.

https://p.dw.com/p/3W8dr
Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey - Mahamadou Issoufou
Hoto: AFP/I Sanogo

 Da safiyar wannan Litinin din ce shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou, ya tashi zuwa birnin Pau na kasar Faransa domin halartar zaman taro na tsakanin shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron da shugabannin kungiyar G5 Sahel kan kasancewar sojojin Faransa na Barkhane a yankin Sahel da kuma yiwuwar sake duba yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen kan harkokin tsaro. Sai dai tafiyar ta Shugaba Issoufou zuwa wannan taro, ya haifar da cece-kuce a kasar bayan kisan gillan da ‘yan ta’adda suka yi wa sojojin kasar 89. 


Tun dai wannan hari na baya-bayan nan da aka kai na garin Chinagodar da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin na Nijar 89, ne jama’a suka soma aza ayar tambaya kan ko Shugaba Issoufou zai samu halartar wannan taro na birnin Pau ko kuma zai kaurace masa. Sai dai a wannan rana ta gabbata cewa shugaban ya tashi a yau din nan wajejen 11 da rabi zuwa 12 ya zuwa kasar ta Faransa inda tare da takwarorinsa za su nemi samun mafita kan rikicin da ke kara kamari a yankin na Sahel wanda a yanzu haka kasar Nijar ta fi ko’ina dandana kudarta dangane da hare-haren ‘yan ta’adda. Kungiyoyin fararan hulla masu nuna adawa da siyasar tsaro ta Faransa a yankin na Sahel sun nuna adawarsu kan wannan taro.

Niger Niamey | G5-Sahelgipfel | Keïta & Issoufou &Kaboré & Déby & Ghazouani
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Suma dai wasu daga cikin ‘yan siyasa ba’a bar su a baya ba wajen caccakar wannan lamari na taron shugabannin na G5 Sahel da shugaban kasar Faransa a birnin Pau na kasar ta Faransa, inda a cewar Soumaila Amadou shugaban Jam’iyyar PND Awaiwaya taron ba shi da wani amfani ga kasar Nijar da ma ‘yan Nijar.

A baya dai sani kowa ne shugaban Kasa Issoufou Mahamadou ya fada cewa nuna adawa ga wadannan abokan hulda da ke dafa wa kasar ta Nijar irin su kasar Faransa da dai sauransu, tamkar nuna goyon baya ne ga ‘yan ta’adda, ganin cewa a koyaushe burin ‘yan ta’addan shi ne na a kori sojojin kasashen na waje daga yankin Sahel. Kuma a cewar Assoumana Mahamadou wani kusa a Jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki mai daki dai shi ya san inda yake yi masa yoyo.


Sai dai kafin ya bar birnin na Yamai zuwa kasar ta Faransa Shugaba Mahamadou Issoufou ya jagoranci wani taro na majalisar koli ta tsaro inda ya kori babban hafsan sojan kasar ta Nijar Janar Ahmed Mohammed tare da maye gurbinsa da Janar Salifou Modi, sai kuma Brigediya Janar Seidou Bague wanda shi kuma aka nada shi a matsayin babban hafsan hafsoshi na sojan kasa. A ofishin ministan tsaro brigediya Janar Didilli Amadou ne aka nada sakatare janar na ofishin wanda ya canji Janar Ibrahim Wally Karingama, Sai kuma brigediya Janar Sidikou Issa wanda shi aka ba shi mukimin babban Speto Janar na sojoji a ofishin ministan tsaron kasar ta Nijar. Abun jira a gani dai shi ne na yadda sakamakon wannan canje-canje da kuma zaman taro na birnin Pau za su ba da wajen kawo karshen kashe-kashen da ‘yan ta’adda ke yi wa sojoji a nan Nijar da ma kasashen Mali, da Burkina Faso.

Belgien Brüssel EU Gipfel | Emmanuel Macron
Hoto: Getty Images/AFP/A. Oikonomou