1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawara kan kasuwanci mara shinge tsakanin Afirka da Turai

April 1, 2014

Batun kulla kawancen kasuwanci tsakanin kasashen Afirka da na Turai ya dade yana daukar hankalin nahiyoyin biyu sai dai babu tabbacin za su cimma matsaya

https://p.dw.com/p/1BZlv
Nkosazana Dlamini-Zuma in Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa

Ranar laraba idan Allah ya kai mu ne ake sa ran shugabanin Afirka da na Turai za su gana a wani taro na musamman da suka shirya a birnin Brussels na kasar Beljiyam. Batun kawancen kasuwanci ne ake sa ran zai kasance kan gaba a batutuwan da shugabanin za su tattauna, sai dai kawo yanzu babu wata alama mai nuna cewa bangarorin za su cimma nasara ko a wannan karon.

A yanzu haka dai kafofin yada labarai sun cika da labaran da suka danganci shugabanin Afirkan da za su halarci taron da wadanda za su zauna a gida.

Kasar Eritrea dai ba ta sami goron gayyata ba saboda rahotanni take hakkin bil adaman da ake yi a kasar, a yayin da shi kuma shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yanke shawarar kauracewa taron duk da cewa shi ne mataimakin shugaban kungiyar tarayyar Afirkar, bayan da mahukutan Beljiyam suka hana mai dakinsa visar raka shi taron.

Shi kuma shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya ce ba zai sami damar halarta ba saboda wani uzurin da ke gaban shi, amma wasu majiyoyi sun ce yana Allah wadai da katsalandan din da Turai take yi wajen tantance wanda ya cancanci ya halarci taron da shugabanin nahiyoyin biyu za su yi.

Slum Schule in Nairobi Kenia
Shugabanin za su tattauna batun illimi a AfirkaHoto: DW/A. Stahl

Zuba jari a al'umma da samar da wadata da zaman lafiya

Ko ma dai me ake ciki, taron na karo hudu ya dauki taken zuba jari a al'umma, da samar da wadata da zaman lafiya. Sai dai tambayar ita ce ko duka kasashen Afirkan za su amince da wannan yarjejeniya ta EPA?

Ita dai wannan yarjejeniya ta EPA ta tanadi duk kasashen da mafi yawan alummominsu ke karbar albashin dake kasa da dalan Amirka 500 a karshen kowace shekara, kuma wadannan kasashen wadanda suka hada da na Afirka da na yankin Karribean na da wa'adin nan zuwa watan Oktoba mai zuwa su bude kasuwanninsu ga kayyakin Turai, su ma kuma su tura na su ba tare da biyan wani kudin kustom ba

Babu shakka mahalarta daga nahiyoyin biyu za su sami damar tattaunawa a tsakaninsu, domin samun moriyar tayin da ke gabansu kamar dai yadda Francisco Mari, wani jami'i daga kungiyar agaji ta Brot für die welt ya bayyana.

Mandela Trauerfeier Johannesburg 10.12.2013
Jacob Zuma ya ce ba zai halarci taron baHoto: Reuters

Tayin shigar da kaya ba tare da kudin kwastam

"Tun a shekara ta 2000 lokacin da aka gudanar da taron Doha wanda ya fi suna, tarayyar Turai tare da hadin gwiwar cibiyar kasuwanci na duniya suka yi wani tayi ga kasashe 40 wadanda suka fi fama da talauci a duniya inda 33 daga cikinsu kasashen Afirka ne, suka ce za su iya tura amfanin gonansu da duk wasu kayayyaki da suke san fitarwa zuwa kowace kasa ba tare da sun biya kudin kwastam ba"

Kawo yanzu dai kasashen Afirka hudu ne kacal suka nuna sha'awar kulla wannan yarjejeniya, Gwamnatocin kasashen na duba tanade-tanaden wannan yarjejeniya dan ganin irin tasirin da zai yi idan har suka bude kasuwannisu wa kayayyakin Turai kuma suna ta tura yin shawarar zuwa baya. Jack Mangala, mallamin kimiyyar siyasa da tarihi da al'adun Afirka a Jami'ar Michigan dake Amirka ya ce kamata ya yi shugabanin Afirka su mayar da batun kan gaba a manufofinsu na siyasa

Kwararru sun ce akwai batun siyasa

North Mara Gold Mine in Tansania
Ma'adinan karkashin kasa na jan hankalin masu zuba jariHoto: DW/J. Hahn

"Ya kamata su sanya batun yarjejeniyar ta EPA a cikin batutuwan da suka danganci siyasa, domin bisa la'akari da bangarin shugabanin Afirka, kamata ya yi su duba yadda zai yi tasiri a manufofin siyasarsu idan har wa'adin watan Oktoban ya wuce ba su sa hannu kan wannan yarjejeniya ba. A ganina na bangarorin biyu zasu amfana daga wannan shiri."

Burin kungiyar ta EU shi ne bayan sun bude kasuwanninsu ta yin amfani da siyasa da ci-gaba, suma sun yi nasarar bude nasu kasuwannin wa Afirka, ta haka za su sami damaryi wa kamfanoninsu hanyar yin takara da takwarorinsu na sauran nahiyoyin a kasuwanni duniya, kamar yadda Alex Vines shugaban cibiyar nazarin Chattam House dake Landan ya bayyana

"Abin da nake sa ran gani daga taro ba yawa, saboda nan ba da dadewa ba za a yi zaben 'yan majalisar dokokin Turai daga nan kuma sai a girka sabuwar hukuma, wannan zai sa a sami sauyi sosai a Brussels kuma shugabanin Afirkan na sane da hakan, saboda haka, a gani na taron ba komai zai yi ba, illa share fagen wanda za su yi a shekara ta 2017"

Idan har tayin na Turai ya sami karbuwa, ba nauorori da sauran kayayyaki ne kadai za su sami shiga ba, har ma da sauran kamfanoni irin na insora, da bankuna, na masu ba da shawarwari.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar