Mahaukaciyar guguwa ta afkawa Yemen | Labarai | DW | 03.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahaukaciyar guguwa ta afkawa Yemen

Dubban mutane ne a kasar Yemen suka kauracewa matsugunansu bayan da wata mahaukaciyar guguwa ta afkawa wasu sassa na kudu maso gabashin kasar.

Hukumomi suka ce guguwar da ke tafe da ruwa mai karfin gaske ta haifar da ambaliya da kuma lalata gine-gine kuma ana fargaba ta samun asarar rayuka da dama.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO) ta ce tuni ta aike da kayan agaji ga wanda wannan lamarin ya shafa kana ta aike da man fatur don yin amfani da su a motocin da ke jigilar mara lafiya.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke fama da rikici tsakanin dakarun da ke biyayya ga gwamnati da kuma wanda ke rajin ganin sun karbe iko da kasar.