Mahamane Ousmane tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar, wanda ya fara lashe zaben shugaban kasa lokacin da kasar ta koma tafarkin demokaradiyya a 1993.
Gwamnatin ta kawo karshe a shekarar 1996 lokacin da sojoji suka yi juyin mulki saboda rudanin siyasa da aka samu. Daga bisani ya zama shugaban majalisar dokokin bayan zaben shekarar 1999.