Mahajjata miliyan biyu sun fara tafiya Mina | Labarai | DW | 24.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahajjata miliyan biyu sun fara tafiya Mina

Hukumomin Saudi Arabiya sun ɗauki tsauraran matakan tsaro tare da kashe sama da Euro miliyan 220, domin tabbatar da gudanar da aikin hajjin bana cikin lumana.

Sama da Maniyyata miliyan biyu ne suka fara shika shikan gudanar da aikin Hajjin bana a wannan larabar a birnin Makkan Kasar saudi Arabiya. Maniyyatan yanzu haka dai sun fara tafiya Minna, domin shirin hawa tsaunin arafat a ranar alhamis. Kusan musulmi miliyan 1.6 suka fito daga kasashen duniya domin gudanar da aikin ibada na Hajji, a yayin da wasu dubu 750, suka fito daga ƙasar ta Saudi Arabiya. Rahotanni na nuni da cewar, hukumomin ƙasar sun ɗauki tsauraran matakai na tsaro, domin tabbatar da cewar an gudanar da aikin hajjin bana ba tare da wata matsala ba. Hukumomin Saudiyya dai sun ɗauki matakai na yi wa birnin na Makka gyaran fuska da inganta wuraren ibada a wani mataki na kauce wa, wanda yaci tsabar kuɗi sama da Euro miliyan 220 a 'yan watannin da suka gabata. Aikin hajji dai shine na biyar kuma cikon shika shikan musulunci da ake muradin ko wane mutum ya aiwatar dashi akalla sau ɗaya a tsawon rayuwarsa, idan yana da zarafin hakan.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu