Magunguna kare kai daga kamuwa da Ebola | Labarai | DW | 26.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Magunguna kare kai daga kamuwa da Ebola

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce a cikin shekara mai kamawa ne za a fara amfani da magnunguna kare kai daga kamuwa da cutar Ebola wadda tai ta'adi mai yawa a Afrika.

Hukumar ta ce za ta maida hankali kan magunguna biyu wanda kamfanin nan na GlaxoSmithKline na Burtaniya da NewLink Genetics na Amrika suka samar kuma ta ce ta na aiki tare da su don ganin an hanzarta kammala yin gwaji kan magugunan.

Mukaddashiyar darakatar Hukumar ta Lafiya ta Duniya Marie-Paule Kieny ta shaidawa manema labarai a Geneva cewar tuni ma an fara gwaji kan maganin da kamfanin GlaxoSmithKline ya samar a Amirka da Burtaniya kana cikin makon gobe ne za yi wani gwajin a kasar Mali.