Magoya bayan Mursi na Zanga-zanga
August 30, 2013Masu aiko da rahotanni sun ce an fara zanga-zangar ce bayan kammala sallar Juma'a a birnin Alkahira da Isma'iliya da sauaran bangarori daban-daban na kasar, inda suke ta rera kalamai na kin jinin sabbin mahukuntan kasar.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Masar din ta ce ta girke jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana a wurare daban-daban na Alkahira da sauran yankunan kasar.
A wani labarin kuma, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun bude wuta kan wani ofishin 'yan sanda a yankin Heliopolis da ke birnin Alkahira da safiyar yau, inda dan sanda guda ya ransa ransa.
Kamfanin dillancin labaran Masar na MENA wanda ya rawaito wannan labarin ya ce baya ga dan sanda da ya rasu, wasu karin mutane ciki har da fara hula sun jikkata a harin wanda ba a san musbbabin kai shi ba.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu