Magana a Makirufo – Yaɗa Labarai da Rahotanni | Learning by Ear | DW | 18.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Magana a Makirufo – Yaɗa Labarai da Rahotanni

default


Shin ka taɓa tunanin ko wane ne ke bayan fage a gidan rediyo ko TV da ka fi ƙauna? A cikin sabon shirin wasan kwaikwayonmu na Ji Ka Ƙaru muna ɗauke da bayani a game da kafofin yaɗa labarai.


Su kan fallasa taɓargaza da kan razana duniya, su kan haɗu da shahararrun mutane masu faɗa a ji kuma nan take su kan hallara a wuraren da abubuwa ke faruwa. Aikin jarida wata sana'a ce mai ban sha'awa, amma kuma tana tattare da haɗari. Wannan maganar kazalika ta shafi wasan kwaikwayo. Misali dai Nijeriya tana da bunƙasar harkar fina-finai kuma da yawa daga 'yan wasan kwaikwayo a ƙasar sun zama abun koyi ga dubban mutane. Amma fa mutane 'yan ƙalilan ne suka san irin wahalar dake tattare da wasan kwaikwayo.

Wannan shirin zai ba ku cikakkiyar dama ta fahimtar ayyukan kafofin yaɗa labarai. Sabon shirin Ji Ka Ƙaru akan kafofin yaɗa labarai da rahotanni zai kewaya da ku masana'antar yaɗa labarai.

Zaku haɗu da Young Junior da Sister P. da Charlie da Ezra a cikin salsala goma na wasanninmu na kwaikwayo ta gidan rediyo a daidai lokacin da suke ƙoƙarin neman sanin yadda ake kafa gidan rediyo da kuma yadda mutum zai cimma nasara a harkar yaɗa labarai. Kama daga kyawawan ɗabi'un da suka shafi aikin jarida zuwa ga gogayya da masu hannu da shuni da masu faɗa a ji. Sai a biyo mu sannu a hankali a sabuwar salsalar guda goma.

Sauti da bidiyo akan labarin